No title


LA'ANANNIYA

Da sunan sarki gwani guda zan yo waƙar la'ananniya 
Allahu Azizu, Al-Karimu mai ikon duka duniya
Ina roƙonka da ka ba musulmai kariya 
Game da waƙi'ar da muke fuskanta a duniya 
Albarkacin baban Fati, Muhammadu mai son gaskiya. 

A yau zan yo raddi wa Kangana la'ananniya 
Jaɓa mai dogon baki jemammiya 
Kin taɓo mu ne dole mu yi miki tofiya
Kuma kin ɗauko hanya ta ɓata wahalalliya 
Tabbas yanzu kin tabbata ke ce wawiya. 

A cikin azamarki ta son ganin kin zam shahararriya 
Kin zamo kunama wacce bata da sabo gantalalliya 
Kin ci zarafin kowa kuma kin ɓata rawarki gaba ɗaya 
Hakan yasa a yau ki ka zamo watsatstsiya 
Baki nan ba ki can ko ina gudunki ake yi mujiya. 

Mai ƙin addininmu tabbas ita ce tsinanniya
Kangana ko kuma ku ce firgitacciya
Ga ta 'yar ƙyamas kamar zane aka ɗaura wa muciya
Sai bala'i ku kira ta masifaffiya 
Mai siffar kanunfari kawai shagiɗaɗɗiya. 

Busashiya, maras tsari wahalalliya 
Munafuka abar gudu annamimiya 
Jakar mata, abar tsana taɓaɓɓiya 
Jemammiya, 'yar bishiya lanƙwasashiya 
Sai zare ido kamar ana yi wa mujiya tsargiya. 

Allahu daɗo daɗin tsinuwa a wurin wannan wulaƙantacciya 
Ja'ira mai ja'irci 'yar jagaliya
Shagiɗaɗɗiya maras kunya karkatacciya 
Maras daraja kamar sosa koɗaɗɗiya 
A wayi gari ta yamushe ko ta zamto tozartacciya. 

Allah ya watsa lamarinki ki zamo tambaɗaɗiya 
Yar maye mai shisshigi makakkiya 
Kin yi asara yar bayan gari makauniya 
Maras hankali kai kuce mata mahaukaciya
In kuma tana da rabo ka sa ta gane gaskiya. 

Allah ga baiwarka ta taɓo addinin gaskiya 
Idan tana da niyyar tuba ka sa ta zamo shiryayyiya 
Idan bata da shi ka sa ta zamo watsatstsiya 
A bita a layi, ko'ina ana ga bushiya 
Kuma cikin gaggawa ka sa ta zamo taɓaɓɓiya. 


©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
  08185819176 
Haimanraees@gmail.com
 

Post a Comment (0)