_*ADDU'A GA "YA"YAN MU.*_
(Mal. Aminu Ibrahim Daurawa).
Wannan Addu'a itace yakamata iyaye maza da mata su dinga yiwa "ya"yansu domin samun zuriyya ta kwarai...
(1) Ya Allah kayi min albarka a cikin 'ya'yana.
(2) Ya Allah kayi masu muwafaka su zamo masu yi maka biyayya.
(3) Ya Allah Ka azurtani da suyi min biyayya.
(4) Ya Allah yadda ka sanar da Annabi Musa ilimi ka sanar da 'ya'yana ilimi.
(5) Ya Allah yadda Ka fahimtar da Annabi Sulaiman Ka fahimtar da 'ya'yana.
(6) Ya wanda Ya ba Annabi lukman hikima. Allah ka Bawa 'Ya'ya na hikima kuma ka basu iya zance.
(7) Ya Allah Ka bawa 'ya'yana ilimin da basu sani ba.
(8) Ya Allah Ka tunatar da su abinda duk suka manta.
(9) Ya Allah Ka budewa 'ya'yana albarkar sammai da kasai.
(10) Ya Allah Kai mai ji ne kuma mai amsawa ne.
(11) Ya Allah ina rokonka, ka bawa 'ya'yana gam da katar na abubuwan alkhairi.
(12) Ya Allah Ka basu karfin hadda, kuma Ka basu saurin ganewa,Ka basu kaifin tunani.
(13) Ya Allah Kasa 'ya'ya na su zamo shiryayyayu, masu shiryarwa.
(15) Ya Allah Kai mai ji ne kuma mai amsawa.
(16) Ya Allah Ka dawwamad da Imanin Ka a cikin zukatan su.
(17) Ya Allah Ka qawata zukatansu da Imani, Ka sa masu kyamar kafircine.
(18) Ya Allah Ka sa masu kyamar fasikanci da kyamar sabon Ka.
(19) Ya Allah Ka sanya su cikin shiryayyayu.
(20) Ya Allah Ka gyara halayen 'ya'yana, Ka cika zukatan su da haske da hikima.
(21) Ya Allah Ka tsarkake zukatan 'ya'ya daga barin riya.
(22) Ya Allah Ka tsare mani gabobin 'ya'yana, Ka kare su daga yin zina,Ka kare su daga yin luwadi,Ka kare su daga yin madigo Ka kare su da dukkan
laifuffuka Ka kare mani zuri'a ta.
(23) Ya Allah Ka sanya 'ya'yana su zamo mahaddatan Al-Qur'ani,su zamo masana Sunnar Annabin Ka (SAW).
(24) Ya Allah Ka azurta 'ya'yana da kamewa da yarda da hukuncin da kayi akan su.
(25) Ya Allah Ka azurta 'ya'yana da kaunar Ka da kaunar Annabin Ka da kaunar duk wanda Kake kauna da kaunar duk wani aiki da zai kusantar dasu zuwa ga samun soyayyar Ka.
(26) Ya Allah Ka budewa 'ya'yana kofar arziki na halal daga mayalwaciyar falalar Ka kuma Ka wadatar da su da halal da barin haram.
(27) Ya Allah ka nisantar dasu daga abokai ko kawaye munana da zasu bata tarbiyyar su ko halayen su Ka raba su da alfasha da dukkan mummunan abu.
(28) Allah kasa 'ya'yana su zama masu lafiya a jikin su, Ka kare masu kunnuwan su,Ka kare masu idanuwan su,Ka kare masu rayukan su,Ka kare masu gabbansu ga barin sa6on ka.
Ya Allaah mai jin qan masu jin qai kasa mudace da rahmarka, ka bamu "ya"yaye nagari daga cikin salihan bayinka, kayi mana kuma jagora acikin dukkan lamuran mu duniya da lahira.
_*ALLAHUMMA AMEEN YA RABBIL ALAMIN*..._
Turawa "yan-uwa da abokan arxuqa domin suma su ammafana da wannan Addu'a mai albarka da fa'ida...