LADAR KOWANE TAKU ZUWA SALLAR JUMA'A
*Kowane taku zuwa Sallar juma'a Ladar aikin Shekara na azumi da tsayuwar dare*
Daga Ausi bn Ausi Assaqfy R.A yana cewa:-
"Naji Manzon Allah ﷺ yana cewa;-
*(Dukkan wanda yayi wanka a ranar juma'a wankan juma'a,Yayi sammankon zuwa da wuri sallar juma'a,ya tafi a kasa bai hau abin hawa ba,ya matsa kusa da Liman ya saurari khuduba,bai yi magana ba,yana da Ladar ko wane taku da yayi zuwa sallar juma'a,ladar azumin shekara da tsayuwar daren shekara)*.
@ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺣﻤﺪ ﻭﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ ﻭﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻟﻌﻼﻣﺔ ﺍﻻﻟﺒﺎﻧﻲ .
Malamai suna cewa;-
"Babu san wani hadisi da yafi wannan Hadisi dauke da lada da falala mai yawa ba kamarsa".
*Ko wane taku yana daidai da ladar azumin shekara guda da tsayuwar dare da ibada na shekara guda,taku daya yana daidai da azumin kwana 365 da ibadar daren kwana 365*.
Yana daga falalar Allah akan bayinsa ya sanyawa aiki dan kadan da lada mai yawa,wannan lada bata samuwa sai ga wanda ya cika sharudda guda biyar kamar yanda hadisi ya tabbatar.
SHARUDDAN SUNE
*1-Yin wankan juma'a*
*2-Tafiya zuwa masallacin juma'a da wuri*.
*3-Tafiya Masallacin a kasa ba akan abin hawa ba*
*4-Halartar Khuduba*
*5-Yin shiru dan sauraran Khuduba*
*-Fuskantar Liman lokacin da yake Huduba*.
Allah ne mafi sani
Dan jin karin bayani game da wannan hadisi zaka iya sauraran babban malami daga cikin manyan malaman duniya a yanzu wato;-
ﺃﺳﻤﻊ ﺍﻟﺸﻴﺦ ﺻﺎﻟﺢ ﺍﻟﻔﻮﺯﺍﻥ
ﻣﺎﺫﺍ ﻳﻘﻮﻝ ﻋﻦ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ
https://m.youtube.com/watch?v=f0XEkO-bWEQ
ﻓﻀﻞ ﺍﻟﺘﺒﻜﻴـــــــــﺮ ﻭﺍﻟﻤﺸﻲ ﻟﺼﻼﺓ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ ﺍﺟﺮ ﻋﻈﻴﻢ ــ ﺍﻟﺸﻴﺦ ﺻﺎﻟﺢ ﺍﻟﻔﻮﺯﺍﻥ
youtube.com