Sahabbai Mu'ujiza ce daga Mu’ujizojin Annabi (ﷺ) (1)

Ramadaniyyat 1442H [11]

Dr. Muhd Sani Umar 

Sahabbai Mu'ujiza ce daga Mu’ujizojin Annabi (ﷺ) (1)


1. Sahabbban Annabi (ﷺ) mu’ujiza ce daga cikin mu’ujizojin Annabi (ﷺ). Domin a tarihin duniya kakaf ba a taba samun wani mutumin da ya zo ya tarar da wata al’umma da ta lalace ta kowace irin fuska ba, amma a cikin dan lokaci kadan da ya zauna tare da su, ya iya samar da gagarumin canji a cikinsu. Wannan shi ne abin da Ma’aiki (ﷺ) ya samar a cikin kabilar Larabawa da al’ummar duniya gaba daya.
2. Akan ji a tarihin manya-manyan mutane masu zuwa domin su kawo gyara a wani bangare na rayuwar al’ummunsu, wani ya zo don kyawo gyara ta bangaren zamantakewar iyali, ko ta bangaren tattalin arziki ko ta bangaren mu’amala, ko bangaren siyasa da shugabanci. Duk da cewa ta bangare guda ne kawai ya zo ya yi gyara a cikinsu, amma sai a ga cewa ya dauki shekaru masu yawa; talatin ko fiye da haka, bai iya samar da canji na a zo a gani ba a cikin wannan al'ummar. Wani ma a cikinsu har zai bar duniya ba tare da canjin ya tabbata ba, sai dai kawai tarihi ya kiyaye cewa, 'wane' ya yi rayuwa a lokaci kaza ya yi fafutukar neman kawo gyara, amma bai ci nasara ba, ko kuma a ce an samu dan canji bayan tafiyarsa, amma ba ta hannunsa ba.
3. Alal misali, Allah (SWT) ya ba da labarin Annabi Nuhu (AS) a cikin littafinsa mai tsarki cewa, ya zauna a cikin mutanensa tsawon shekara dubu ba hamsin, amma tare da haka, ba a samu wadanda suka yi imani da shi ba sai ‘yan tsirarun mutane. Allah (SWT) ya ce: (Ba kuwa wadanda suka yi imani da shi sai ‘yan tsirari.) [Hud: 40]
4. Hakanan Annabi Ibrahim (AS) shi ma Allah (SWT) ya bayar da labarin irin gwagwarmayar da ya sha da mutanensa a Iraki, tun kafin ya yi hijira ya dawo kasar Sham da zama shi da iyalansa, wanda ta kai har mutanensa suka yi yunkurin hallaka shi ta hanyar kona shi da wuta, Allah (SWT) ya tseratar da shi. Tare da haka Allah (SWT) bai fadi cewa al’umarsa ta musulunta ba. Abin da Allah ya ce dangane da wadanda suka yi imani da shi shi ne: (Sai Ludu ya yi imani da shi. (Sai Ibrahimu) kuma ya ce: “Lalle ni mai yin hijira ne zuwa ga Ubangijina; lalle Shi Mabuwayi ne, Mai hikima.”) [Ankabut: 26]
Wanda shi ma dan dan’uwan Annabi Ibrahimu ne ko dan baffansa. Sai kuma matarsa Sara. 
5. Wannan ce ta sa shi dole ya fita ya bar kasarsa, ya yi hijira zuwa kasar Sham, inda a nan ne ya kafa zurriyarsa wadda Allah (SWT) ya fitar da annabawa masu yawa daga cikinta. 
6. Duk da matsayin da Annabi Ibrahim (A.S) yake da shi a wurin Allah SWT), wanda har Allah ya rike shi a matsayin Badadiyinsa, amma har ya bar duniya bai iya kawo wani gagarumin canji a cikin al’umarsa ba. Haka ya koma ga Allah ba tare da wannan nasara ta tabbata a hannunsa ba.
7. Hakanan Allah (SWT) ya ba da labarin Annabi Yusuf (A.S) a cikin Alkur’ani mai girma, da irin wahalhalun da ya sha har aka kawo shi Masar aka sayar da shi a matsayin bawa, da shigarsa kurkuku da fitowarsa da zamowarsa babban Firaminista a kasar Masar. Tare da duk wannan, Allah yana ba da labari bisa harshen muminin gidan Fir’auna lokacin da yake jan hankalin mutanensa da cewa: (Hakika kuma Yusufu ya zo muku da (hujjoji) bayyanannu tun kafin (zuwan Musa), sannan ba ku daina zama cikin kokwanto game da abin da ya zo muku da shi ba har yayin da ya mutu sai kuka ce: “Allah ba zai sake aiko da wani manzo bayansa ba.” Kamar haka ne Allah Yake batar da duk wanda shi mai barna ne, mai shakka.) [Ghafir: 34]
8. Wannan aya ta nuna cewa Annabi Yusuf (A.S) ya gama zamansa a kasar Masar, tare da dukkan matsayin da ya rike da abubuwan da aka gani a wurinsa masu nuna gaskiyarsa, amma bai samu nasarar shigar da wasu cikin addinin Musulunci ba.

Zai Ci Gaba Insha Allah.
Post a Comment (0)