BANA SO NA SHA AZUMI, KO ZAN IYA SHAN MAGANIN HANA HAILA ?

*BANA SO NA SHA AZUMI, KO ZAN IYA SHAN MAGANIN HANA HAILA ?*



 *Tambaya*

Assalamu alaikum, 
Allah ya gafarta malam, azumi ya zo ni kuma ba na son na sha ko azumi daya, to shi ne na sayi maganin da zai hanani yin al'ada na sha, bayan mun hadu da kawata, sai take ce min wai babu kyau, shi ne na ce mata ban yarda ba, zan tambayi malamai, don Allah malam a kara min haske ?


*Amsa*

Wa'alaykumussalam, 
To 'yar'uwa amfani da maganin da yake hana haila ya halatta, Idan ya zama ba zai cutar ba, amma idan zai cutar, to ya haramta saboda fadin Allah “kar ku jefa kawunanku a cikin halaka” suratu Albakarah aya ta 195. Saidai duk da cewa hakan ya halatta da sharudan da suka gabata, amma barinsa shi ya fi, sai idan bukatar hakan ta taso, saboda mutum ya zauna akan yadda yake ya fi masa kwanciyar hankali akan ya yi abin da zai canza dabi’arsa, musamman ma wasu daga cikin kwayoyin na zamani suna dagula kwanakin haila, kamar yadda ya bayyana gare mu, sai a kiyaye.Don neman karin bayani, duba : Dima'uddabi'iyya shafi na : 54 .

Allah ne mafi sani.

*Amsawa*✍🏻

*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*

22\6\2015

Zaku iya bibiyar mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)