SAI MU YI TA ADDU’A AMMA A KI AMSA MANA


*SAI MU YI TA ADDU’A AMMA A KI AMSA MANA* 

Babban bawan Allah nan Ibrahim al Adham ya zo wucewa ta cikin kasuwar Basrah, sai mutane suka taru suka ce masa: Me yasa sai mu yi ta addu’a amma a ki amsa mana, alhali Allah (SWT) ya ce: “Ku roke ni in amsa muku” (Bakarah) sai ga shi mun dau tsawon lokacin muna addu’a an ki amsa mana? 
Sai Malam Ibrahim al Adham ya ce: “Saboda zuciyarku ta mutu a abubuwa goma, shi ya sa ba a amsa muku; 

1. Kuna sane da Allah, amma ba ku ba da hakkinsa ba, 
.
.
2. Kun karanta Alkur’ani, amma ba ku yi aiki da shi ba,
.
.
3. Kuna da’awar son Annabi (SAW), amma kun kyale sunnarsa, 
.
.
4. Kuna da’awar gaba da Shaidan, amma kuke biye masa, 
.
.
5. Kun ce kuna son aljanna, amma kun ki yin aiki don ita, 
.
.
6. Kun ce kuna tsoron wuta, amma kuka kai kanku gareta, 
.
.
7. Kun ce mutawa gaskiya ce, amma ba ku yi mata tanadi ba, 
 
.
8. Kun shagalta da duban aibin ‘yan uwanku, kun manta da naku, 
.
.
9. Kun sami ni’imar Allah, amma ba ku gode maSa ba, 
.
.
10. Kun binne matattunku, amma ba ku wa’azantu da su ba.

Daga
Miftahul ilmi

ZaKu iya Bibiyar Mu a 

Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
Post a Comment (0)