SUNAN ALLAH AKE SO KAFARA AMBATA LOKACIN DA KA TASHI DAGA BARCI



SUNAN ALLAH AKE SO KAFARA AMBATA LOKACIN DA KA TASHI DAGA BARCI

Babban guri da alfaharin Shaidhan da masu taimaka masa shine suga sun halaka dan Adam ya mutu ya shiga wuta kamar yadda suma suka halaka,Shiyasa yake bibiyayyar lokuta mafi tsada dan halaka dan Adam,kamar lokacin kwanciya barci ko lokacin tashi daga barci.

 SHAIDHAN YANA YIN KWALLI GUDA UKKU LOKACIN BARCINKA

Annabi SAW yana cewa:
*(Shaidhan yana yin kwalli guda ukku a daidai kan dan Adam lokacin da yake kwance yake barci,ko wane dauri yana rudarka da cewa akwai sauran dare mai yawa, amma idan ka ambci Allah lokacin tashi daga barci sai dauri daya ya since,idan kayi alwala sai wani daurin ya since, idan kayi sallah sai sauran dayan ya sinci sai ka wayi gari cikin nishadi da walwala da jin dadi, amma idan bakayi haka ba sai ka wayi gari cikin damuwa da kasala da bakin ciki)*
@ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﻭ ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ.

Imam Nawawy Allah yayi masa rahama yana cewa:
"Abinda zahirin wannan hadisi yake nuna mana dukkan wanda bai hada wadan nan abubuwa guda ukku wato ambaton Allah sannan alwala sannan Sallah lokacin tashi daga barci, to yana cikin wadanda zasu wayi gari cikin bacin rai da damuwa da kasala".
 @ﺷﺮﺡ ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ( ٦٧ / ).

 
Allah ka bamu ikon aiki da wannan sunnah.
Post a Comment (0)