ABUBUWA GUDA 20 NA SAMUN GYARAN ZUCIYA
1-Yawaita karantun alqurani mai girma,da Kokarin sani ma'anoninsa da kokarin yin zikirai da suka tabbata daga Annabi Muhammad ï·º.da kuma bin sunnar Manzon Allah ï·º.
2-Rage cikin abinci da yawa,ka riqa cin abinci iya buqata.
3-Yawan sallah dare da yawaita ibada cikin dare lokacin da mutane suke barci.
4-Rokon Allah ya gyara maka zuciyarka tare da yin adduar alokacin amsa addua da guraren amsa addua.
5-Zama tare da mutanan kirki dan su tunanatar dakai Allah da jin nasiha da wa'azi daga wajansu da kuma yin koyi da kyawawan halayensu.
6-Yawaita hiru idan zakayi magana kuma ka fara yin tunanin matsayin maganar kafin ka furtata.
7-Nisantar sabon Allah da nisantar masu sabon Allah da nisantar zama tare da su.
8-Yin kokarin cin Halal da amfani da dukiyar halalal da nisantar cin haramun da shubuha.
9-Ka nisanci abubuwan kyama da abubuwa masu halakarwa kamar yi da mutane da shirka da sabawa mahaifa da sauran miyagun halaye.
10-Ka yawaita aiyukan nafila bayan ka sauke farilla,da kuma yawaita nafila kala kala.
11-Yawaita Azumin nafila da bibiyar aikin hajji da Umara.
12-Yiwa kanka hisabi lokacin kwanciyar barci akowane rana da yin hisabin rayuwa gaba daya.
13-Ka sani lallai Allah yana sane kuma yana kallonka duk lokacin da zakayi wani aiki.
14-Kyautatawa mahaifa tare da yi masu biyayya.
15-Yawaita zuwa ziyara maqabarta dan tuna lahira.
16-Yin sadaka ga marayu da masu karamin karfin da gajiyayyu,musammman ma alokacin kuncin rayuwa.
17-Ziyarar duba marar lafiya dan yi masa addua da daukar darasi.
18-Kiyaye Salloli akan lokacinsu kuma acikin jam'i.
19-Yin tunani acikin halittun Allah madaukakin sarki.
20-Nisantar zalumci
Allah ne mafi sani.
.