DARASIN MU NA YAU ZAI MAGANA NE AKAN GIRMAN KAI WANDA HAUSAWA SUKECEMAWA RAWANIN TSIYA
MALLAMIN MU AKAN WANAN MAUDU'IN NA YAU SHINE Yezeed Abdulbasir Maikawo
MUNA KAWOMAKU WANAN KARATUN NE SABIDA GYARAN TARBIYAMU DA SIYASARMU SABIDA MUSAN SUWA ZAMUBI A SIYASA MATSAYIN IYAYEN GIDA YAZAMA WAJIBI MUSAN WANAN KAMAR YADDA YAZAMA WAJIBI MU SHIGA SIYASA.
Assalamu alaikum warahmatullah. Dukkan godiya da girmamawa Suntabbata ga Allah, tsira da aminchin Allah su tabbata ga Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallam.
Bayan haka, Darasin mu na Yau zai magana akan Girman kai (الكبر).
A harshe yana nufin jiji da kai, Alfahari.
A musulunci shine : Kin gaskiya, kauda kai/ kyamatar gaskiya da ganin cewa kafi ƙarfin amsar gaskiya.
Azzabiidii ya fassara da:
حالةٌ يتخصَّص بها الإنسان من إعجابه بنفسه، وأن يرى نفسَه أَكْبَر من غيره.
" Hali/ Ɗabi'ace da Ɗan adam yake ke ɓantuwa dashi, na burge kansa da kansa, kuna yarinƙa gani yafi kowa.
Hadith Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya fassara shi kamar haka;
حديث النبي صلّى الله عليه وسلّم فقد قال: "الكِبْر بطر الحق، وغمط.
Wannan dabi'a ce wadda shaidan yafara siffanta da ita kuma shine Zunubi na farko a duniya bayan halittar Annabi Adam (A.S) . Ga abinda Allah ya fada acikin Qur'an mai Girma.; قل تعالى: ﴿إِذْ قَالَ رَبُّكَ لِلْمَلَائِكَةِ إِنِّي خَالِقٌ بَشَرًا مِن طِينٍ * فَإِذَا سَوَّيْتُهُ وَنَفَخْتُ فِيهِ مِن رُّوحِي فَقَعُوا لَهُ سَاجِدِينَ * فَسَجَدَ الْمَلَائِكَةُ كُلُّهُمْ أَجْمَعُونَ * إِلَّا إِبْلِيسَ اسْتَكْبَرَ وَكَانَ مِنْ الْكَافِرِينَ * قَالَ يَا إِبْلِيسُ مَا مَنَعَكَ أَن تَسْجُدَ لِمَا خَلَقْتُ بِيَدَيَّ أَسْتَكْبَرْتَ أَمْ كُنتَ مِنَ الْعَالِينَ * قَالَ أَنَا خَيْرٌ مِّنْهُ خَلَقْتَنِي مِن نَّارٍ وَخَلَقْتَهُ مِن طِينٍ *
Fassara " Lokacin da Allah yacewa Mala'iku nizan hallita mutum daga Diin ( kasa), Idan na halitta shi, na busa masa ruhi(Rai) sai kuyi masa sujjada, Sai Mala'iku sukayi sujjada dukkansu, Sai shaidan yayi girman kai, (الكبر) ya kasance daga cikin kafirai,
Sai Allah yace yakai Iblis miya hanaka sujjada ga abinda na halitta da hannuna, ................" Zuwa karshe.
Zamu fahimci cewa Shaidan yayi Girman kai ga Allah yana ganin cewa yafi Adam saboda anhaliccesa daga Wuta, Adam daga Din ( kasa).
GIRMAN kai mummunan dabi'a ce wadda ta ke dukkan musulmi ya kaurace mata ya nisanta kansa da ita Allah yabamu ikon kiyayewa.
Akwai Hadith Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam.
وعن ابن مسعود قال: قَالَ رسول اللَّه صَلَّى اللَّه عليه وآله وَسَلَّم: لا يدخل الجَنَّة من كان في قلبه ذرة من كِبْر، فقَالَ رجل: إن الرجل يحب أن يكون ثوبه حسناً ونعله حسناً، قال: إن اللَّه جميل يحب الجمال، الكِبْرُ بَطَرُ الحق وغَمْطُ الناس.
" Baya shiga aljanna wanda yake da kwatankwacin kwayar zarra na girman kai a zuciyarsa, sai wani mutum yace' waninnu yanaso yasa tufafi da takalmi masu kyau ''
Sai yace Allah kyakykyawane kuma yanason mai kyau . GIRMAN kai Ƙingaskiya ne ,kuma kin mutane ne..
وعن أبي هريرة رضي الله عنه، قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: ((ثلاثة لا يكلِّمهم الله يوم القيامة، ولا يزكِّيهم، ولا ينظر إليهم، ولهم عذابٌ أليم: شيخ زان، وملك كذَّاب، وعائلٌ مستكبر "
" Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam yace: Mutum ukku Allah bazai masu maganaba kuma bazai masu maganaba, kuma sunada azaba mai raɗaɗi :
1. Dattijo Mazinachi
2. Mai Mulki maƙaryachi
3. Talaka mai Girman kai.
Lallai Girman kai yana daga cikin laifukan dasu sabbabawa mai aikata shi shiga wutar Jahannama.
قال تعالى: وَلَا تَمْشِ فِي الْأَرْضِ مَرَحًا "
Suratul Isra'i Allah yace" .....Kada ka rinƙa tafiya a ban ƙasa kana Mai jiji da kai........"
قَالَ الله تَعَالَى: تِلْكَ الدَّارُ الْآخِرَةُ نَجْعَلُهَا لِلَّذِينَ لَا يُرِيدُونَ عُلُوًّا فِي الْأَرْضِ وَلَا فَسَادًا وَالْعَاقِبَةُ لِلْمُتَّقِينَ.
Allah yace" Wanchan Gidane na Karshe(Aljanna) wanda mukasashi ( Tana jeshi) ga wadanda basa nufin Girman kai/ son girma da ganin sunfi kowa, kusama basa nufin Fasadi, Makoma tagari tana ga masu jin tsoran Allah."
DALILAN DA KESA GIRMAN KAI
Nadaga cikin abubuwan da kesa mutum girman kai.
1. Girman kai saboda Ilmin da Allah yabaka, na zamani ko na addini.
2. Girman kai saboda Nasba, ( Family status)
3. Girman kai saboda Dukiya ( Wealth)
Kadan daga cikin abubuwan da ke sa girman kai Allah yabamu kariya daga wannan mummunar siffa yakaremu yakare mana imanin mu, yakaremu daga Riya da ayyuka domin riya, ya tabbatar mana da imaninmu, ya Gafartawa mana da iyayenmu da sauran Musulmai .
Ya Allah ka kawomana da zaman lafiya a garuruwan mu da kasarmu baki daya.
Ya Allah kabamu Shuwagabannin kirki, kaza ɓamana ya Allah.
Ya Allah kabawa Matasanmu Ayyukan dogaro da kansu kahanamu maula da banbaɗanchi.
Ya Allah kasama kasuwar mu Albarka, kahada kawunanmu da sauran Musulmai.
Ya Allah kayiwa Jihar Katsina Albarka katsareta da Tsarewarka .
Idan anga kuskure agyara wanda yake dai dai daga Allah ne.
Wasalallahu Wasallim Ala Nabiyyuna Muhammad wa alihi Wasallam.
Subhanakallahumma wabi hamdika Ash hadu Allah lailaha illa anta astagfirka wa atubu ilaik.
Wallahu A'alam.
✏️ . Abou~Haneeph Yazid Abdulbasir Maikawo
Malamin #inuwalikemindsreformational Agenda #inuwalikeminds #inuwalikeminded