KA KIYAYE HARSHENKA



KA KIYAYE HARSHENKA.

Ibnul Qayyim Allah ya masa rahama yana cewa "Yana daga cikin abun mamaki zakaga mutum yana masa sauki ya kiyaye kansa daga cin haram, yin zalunci, aikata zina, yin sata, shan giya, kallon haramun dama wasun wadannan manyan laifukan (abune mai sauki awurinsa ya kiyaye kansa daga aikata su) amma kuma sai yazama abu mai wahala agareshi ya kiyaye *Harshen sa*. 
      Wani lokaci zakaga har nuna wani mutum akeyi ana cewa yanada addini da zuhudu da yawan ibadah, amma zaka sameshi yana wasu maganganu da zasu jawo masa fushin Allah amma ko ajikinsa, wanda kalma daya daga cikin wadannan kalmomin zata iya dulmuyar dashi gwargwadon nisan tsakanin gabar da yamma.
      Sau dayawa zakaga mutum yanada tsantseni wurin aikata alfasha da zalunci amma zaka samu ya sake linzamin harshensa wurin cin mutunci da zarafin rayayyu dama matattu batare da kuma ya damu ba".

الداء والدواء ١/٣٦٦،٣٦٧
#Zaurenfisabilillah

Telegram:
https://t.me/Fisabilillaaah

Instagram:
https://www.instagram.com/zaurenfisabilillah/
Post a Comment (0)