MATA KUJI TSORON ALLAH, KUNE TUSHEN KOWACE ANNOBA.
Ibnul Qayyim Allah ya masa rahama yana cewa "Babu shakka cewa samun dama da Mata sukayi na chakuduwa da maza shine asali da tushen kowane sharri da bala'i, kuma shine mafi girman dalilan saukar uquba, kamar yadda shine dalilin gurbacewar al'amura, haka zalika shine dalilin mutuwar gama gari da saukar Annoba mai halakarwa.
Alokacin da karuwa tasamu daman cudanya da wani soja na Annabi musa, alfasha ta faru atsakaninsu alokacin Allah ya turamusu Annoba a take mutum dubu saba'in (70,000) suka mutu, wannan kissace sananniya acikin littatafan tafsiri.
Daga cikin manyan dalilan mutuwa gama gari shine yawaitar zina, saboda samun daman chakudedeniya tsakaninsu da maza, da yawo atsakaninsu babu lullubi suna masu bayyana adonsu agaresu, wallahi da ace shuwagabanni sun san abunda hakan ke haifarwa na gurbacewar rayuwar civilians kafinma azo batun gurbacewar addini da sun kasance masu daukan mataki mai tsanani wurin hana hakan".
الطرق الحكمية ١/٧٢٤
#Zaurenfisabilillah
Telegram:
https://t.me/Fisabilillaaah
Instagram:
https://www.instagram.com/zaurenfisabilillah/