*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*
*_Me Yake Janyo Yawan Zubar Da Ruwa A Gaban Mace?_*
Yawan zubar da ruwan zai iya kasancewa na cuta ko kuma wanda ba na cuta ba.
*_Abubuwan Da Suke Janyo Zubar Da Ruwa Ba Na Cuta Ba_*
* Juna Biyu (ciki): Amma fa wani lokacin, juna biyu yana iya janyo zubar ruwa na cuta.
* Yin amfani da kwayoyin tsarin iyali lokacin jinin al’ada.
*_Abubuwan Da Suke Janyo Zubar Ruwa Na Cuta_*
* Shan magunguna barkatai, musamman waÉ—an da ake kira da antibiotics ko steroid da sauran su.
* Cututtuka a jiki kamar Diabetes (ciwon suga), HIV, Cancer da sauransu.
* Juna biyu (ciki): yana iya janyo zubar ruwa na rashin lafiya da kuma wanda ba na rashin lafiya ba.
* Saduwa da wanda ya ke dauke da cutar: namiji zai iya dauka daga wurin mace, sannan mace ma zata iya dauka daga wurin namiji. Zinace zinace.
* Yawan wanke cikin gaba da wani sinadari (vaginal douching).
* Masan tangaran (toilet seats): Musamman idan wadda take dauke da cutar ta yi amfani da shi kuma bata wanke masan ba. Amma fa har yanzu ba’a tabbatar da wannan hanyar ba.
Wabillahi Taufiq.
Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*
Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*
*- Zauren Macen Kwarai-*
*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai su tura da cikeken sunansu tare daga in da take, ta wa'innan numba;* 👇 👇 👇
08162268959,08038902454