Ramadaniyyat 1442H [24]
Dr.muhd Sani Umar
Sahabban Annabi (ﷺ) Kakaf Babu Munafuki (4)
_______________________________
1. Za mu iya tabbatar wa da mai karatu cewa, Musulunci tun kafin Fat'hu Makka ya yi nasarar cire kowace irin shirka da ko kowace tatsuniya daga zukatan dukkan masu hankali daga cikin Kuraishawa, dan abin da ya yi saura na taurin kai tare da wasu, shi ma ya zo karshe bayan Fat'hu Makka. Dukkansu suka shiga Musulunci, addinin da tuni ya riga ya sami gurbin zama a zukatansu.
2. 'Yar damuwar da ta yi ragowa kuwa a zukatan wasu daga cikin shugabanninsu, ita ma Annabi (ﷺ) ya yi nasarar kawar da ita ta hanyar yawan kyautata musu da ya yi ta yi, kamar yadda ya fifita su a wajen rabon ganimar yakin Hunainu bayan Fat'hu Makka. Hakanan ya ci gaba da kyautata mu'amalarsu har ya cire duk wata damuwa daga zukatansu.
3. Sannan kuma sai abin da ya biyo baya na tirjiya da aka samu daga Ansar, watau mutanen Madina a kan lamarin halifanci bayan Manzon Allah (ﷺ) wanda daga bisani shi ma aka tabbatar wa da Kuraishawa wannan hakkin ba tare da an kebance shi da wani gida a cikinsu ba. Wannan ya kara wa duk wani mutum bakuraishe kaunar Musulunci a ransa, domin kuwa yanzu ba kasar Makka ce kawai suke da iko da ita ba, a'a suna da iko da wurare masu yawa a bayan kasa. Musulunci ya mayar da su shugabanni na duniya da lahira.
4. Abin da zai kara nuna maka cewa, Musulunci ya yi karfi a zukatansu shi ne, ka dubi yadda wadanda suka fi kowa kafewa da tirjiya har zuwa lokacin Fat'hu Makka, su ne kuma daga baya suka zamanto cikin wadanda suka fi kowa sadaukar da kai wajen jihadin yada Musulunci, kamar irin su Suhailu dan Amru, da Ikrima dan Abu Jahl da baffansa Harisu da Yazidu dan Abu Sufyana.
https://t.me/miftahul_ilmi