No title

🌹 *SOYAYYA* 🌹


Ka karanta har karshe akwai darasi....

*ALBASA* suna son juna ita da *MAN GYADA* wata rana soyayya ta yi dadi sosai sai aka shiga tattaunawa kamar haka:

*MAN Gyada*: Masoyiyata Albasa, ina so ne mu kara kawata soyayyar dake tsakanin mu ne.

*Albasa*: To masoyi na, kamar ya kenan kake nufi kuma ya kake ganin za ayi?

*Man Gyada*; Ai abu ne mai sauki wannan, kawai so nakeyi ne mu tattara inamu-inamu mu koma saman wuta 🔥 domin ina ganin acan ne za mu cancanci sunan mu na Masoya saboda soyewa za mu rika yi gaba daya.

*Albasa*: Kai kai kai .... saman wuta fa kace? Ni dai gaskiya ina jin tsoro kar naje na Qone ko ma na babbake gaba daya na tashi daga aiki.

*Man gyada*: Kayyasa...karki zama kamar yar kauye mana, a ina kuka taba jin ance man gyada da Albasa sun qone? Sai dai su soye 😍

*Albasa* dai ta amince ta bi Man gyada, suka hau kan wuta🔥kuwa ana ta soyewa, tafiya ta yi tafiya sai ga Albasa nan ta Qone kurumus, 

Abin takaicin ma ashe bata sanar da Mahaifinta *ALHAJI RUWA* irin alaqar da ke tsakanin ta da *MAN GYADA* ba, sai kawai ganin albasa akayi ta zama wata iri ta tashi daga aiki....

Lallaikam Albasa batayi halin mahaifinta ruwa ba.

Gani ga wane..

Dan uwanku:

✍🏻 *Idris M Rismawy Abu Nu'aym*
Post a Comment (0)