UWA TA GARI TUSHEN TARBIYYAH
An tambayi yara kan cewa Kowa ya fadi abinda yake so ya zama idan ya girma ?
Wani yace mai tuqa jirgi, wani yace likita, wani yace injiniya dukkansu amsoshin su baya wuce nan. sai dai daya daga cikinsu sai ya fadi bakon abu. Sai dalibai sukayi masa dariya.
Kunsan me ya fada?
Yace : ina son na zamo Sahabi., malamin yayi mamakin dalibin. sai yace danme kake son zama Sahabi?
Sai yace
Mamana kullum kafin na kwanta tana bani labarin sahabi. Sahabi yana son Allah, yana son Manzon Allah, yana biyayya ga Umarnin su. Ina son na zamo irinsa.
Sai malamin yayi shiru.
Yana qoqarin hana hawayen sa zuba saboda wannan amsan. yasan lallai bayan wannan yaro akwai Uwa mai girma, ta gari.
Saboda hakane burinsa ya zama mai girma.
Daya daga cikin Malaman tarbiyya tana cewa wata ran...
Na nema daga gun daya daga cikin azuzuwan primary suyi
min zanen dausayi (cikin damina ).
Sai wata daliba tazo ta zana Al'qur'ani sai nayi mamakin zanenta.
Sai nace ki zanamin dausayi ba qur'ani ba, baki fahimta bane?!
Amsarta kadan ce, bayyananniya kaman takadda agani na ...
Tace : qur'ani shine dausayin zuciyata, hakanan Mamana ta koyamin !
Wace tarbiyya ce waccan?!
Saifullahil maslul Khalid bin Walid idan ya dauki Alqur'ani sai ya shafe shi yana kuka yana cewa( jihadi ya shagaltad damu ga barin ka) me yakai wannan uzurin kyau?
Amma yanzu ( ababen kallo sun shagaltad damu ga barin ka)
Banbancin su harafi ne wane harafu!!
Shin sakon ya cancanci a karanta shi kuma a turashi?
(Eh) ko (A'A)?
Idan eh ne to kada ka ajiye ta ka tura ma mafi darajan mutane a gunka minti daya daga rayuwarmu . .
Numfashi ne wanda bazai dawo ba .. to ka kasance kana yiwa Allah da'a....