WASIYYA AKAN KIYAYE MAFI GIRMAN HAKKIN ALLAH DA HAKKIN BAYIN ALLAH
Mafi girman hakkan Allah bayan hakkin kaɗaita shi a cikin bauta, babu hakkinsa mai girma da yakai JIN TSORON ALLAH DA KIYAYE DOKOKIN ALLAH, Mafi girman hakkin mutane shine KAYI MU'AMALA DA MUTANE DA KYAWAAN HALI NA KWARAI.
Manzon Allah ﷺ yana cewa:-
(Kuji tsoron Allah ku kiyayya dokokin Allah, ku riƙa bin bayan mummunan aiki da kyakkyawan aiki, sai kyakkyawan aikin ya goge mummunan aikin, kuma kayi mu'amala da mutane da kyawawan ɗabi'u)
@حسن - الألباني - صحيح الترغيب (٣١٦٠).
ابن عثيمين رحمه الله:
Yana cewa:-
"Wasiyoyi guda biyu masu girma ta farko kyautata mu'amala tsakanin mutum da Ubangijin sa,ta hanyar bin dokokin sa da jin tsoron za,ta biyu kyautata mu'amala tsakanin bawa da bawa ta hanya sakin fuska da saukin hali da afuwa da sauran halaye na kwarai".
@شرح رياض الصالحين (١/٤٨٦).