Ahlul Fatarat



Tambaya
:
Inason ƙarin bayani a gamed makomar al'ummar da ake ce mata ahlul fatarat. Wato mutanen da suka rayu kafin bayyanar Annabi?
:
Amsa:
:
Haƙiƙa an samu rgāɓānin Mālamai dangane da makomar Mutānen da suka rayu ba tare da an aiko musu da wani Manzo ba, wato waɗanda akafi saninsu da sunan (AHLUL FATRA). da kuma mutanen da har sukayi rayuwarsu suka gama ba su taɓa jin labārin addinin muslunci ba balle su shiga wato irin mutanen da da'awar muslunci ba taje garesu ba har suka mutu, sannan da 'ya'yan kāfirai waɗanda suka mutu tun kafin sukai ga balaga?
:
Mālamai sunyi maganganu dabam-dabam dangane da wannan mas'ala, sannan an samu Hadisai da yawa akan haka, ko da yake daga cikinsu akwai Hadisan da suka inganta akwai kuma waɗanda basu inganta ba balle ayi hujja da su. Danhaka daga cikin Mālamai akwai waɗanda sukace dukkansu za a kaisu gidan Aljanna ne, yayin da wasu Mālaman kuma sukace a'a gaba ɗayansu za a kaisu gidan wuta ne.

Sannan akwai Mālaman da suka raba abin gida biyu, sukace za a sa wasu a wuta kuma a sa wasu a aljanna, Mālaman da suka tafi akan wannan fahimta sukace a ranar Alƙiyama Aʟʟαн(ﷻ) Zai yi musu jarrabawa ne, zai kusanto da wuta sai ya umarci waɗannan mutane da cewa duk su shiga cikin wannan wutar, danhaka duk wanda yayi biyayya da umarnin Aʟʟαн(ﷻ) ya shiga to wutar ba za ta ƙōnā shi ba, sai dai za ta zama mai sanyi da aminci ne a gareshi. Amma waɗanda su ka ƙi bin umarnin Aʟʟαн(ﷻ) su ka ƙi yarda su shiga cikin wutar to shikenan sū ne waɗanda za a yiwa azāba da wutar sakamakon sāɓāwa umarnin Aʟʟαн(ﷻ) da sukayi.
:
Sai dai wasu daga cikin Mālamai kamar irin su:
Ibn-Abdul-Barr,
suna ganin cewa babu wata jarrabawa da za a yi musu a lahira, domin lahira gida ne na sakamakon ayyuka kawai bawai gida ne na umarni da kuma hani ba. To sai dai wasu Mālaman sunyi masa raddin wannan magana, sukace eh alal-haƙiƙa an yarda cewa lahira ba gida ne na umarni da hani ba, to amma sai dai hakan zai kasance ne yayin da aka kammala hisābi 'yan aljanna suka shiga aljanna, 'yan wuta suka shiga wuta, amma a filin alƙiyāma kafin a kammala hisābi za a yiwa wasu jarrabawa kamar yadda tun a cikin ƙabari a kan yi wa mutum jarrabawa ta hanyar yi masa tambayoyi, kamar yadda a ranar alƙiyāma za a ūmarci al'umma su wuce ta kan sirāɗī.
:
Amma dangane da abinda ya shafi mahaukata waɗanda suka ƙare dukkan rayuwarsu ba tare da hankaliba, wasu daga cikin Mālamai sukace nan take za a shigar da su aljanna, amma maganar da tafi inganci itace, suma hukuncinsu ɗaya da waɗancan (Ahlul fatra) ɗin, danhaka suma za a yi musu jarrabawa ne wanda ya cinye wannan jarrabawar a sa shi a aljanna, wanda kuma ya faɗi a jarrabawar sai a sa shi a wuta, Ya Aʟʟαн(ﷻ) kayi mana tsari da wuta amin.
:
※(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)※
:
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
              Daga Zaυren
             Fιƙ-нυl-Iвadaт
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
           Mυѕтαρнα Uѕмαи
              08032531505
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє ғαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι ""lιкє""👇🏾
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/
Post a Comment (0)