Babbar Ni'imar Allah Ga Sahabban Annabi (ﷺ) (2)



Ramadaniyyat 1442 [19]

Dr. Muhd Sani Umar (hafizahullah)

Babbar Ni'imar Allah Ga Sahabban Annabi (ﷺ) (2)
_____________________________

1. Lokacin da wasu daga cikin kabilun Ausu da Khazraju suka je aikin hajji irin ta su ta lokacin jahiliyya, sai suka jiyo Annabi (ﷺ) yana kira zuwa ga Musulunci, sai suka karbi addinin Musulunci suka musulunta. Bayan sun koma gida, shekara mai zuwa sai suka dawo da wasu daga cikin mutanensu sun musulunta, kimanin mutum saba’in (70). Suka hadu da Annabi (ﷺ) suka tattauna, haduwar da ake kira da Bai’atul akba ta biyu, suka yi yarjejeniya a kan cewa, Annabi (ﷺ) zai yi hijira ya koma Madina, su kuma za su taimka masa, za su ba shi kariya da dukkan abin da suke ba wa ‘ya’yansu da matansu kariya da shi. Annabi (ﷺ) ya yarda da wannan ya yi Hijira.
2. Zuwan Annabi (ﷺ) Madina ya sa wadannan kabilu guda biyu suka hade suka zama kamar kabila guda daya, suka koma suna son junansu, suna taimakon junansu kamar wani abu bai taba shiga tsakaninsu ba.
3. To wannan abu da ya faru babu shakka ba zai yi wa yahudu dadi ba, ganin yadda suke cin karensu babu babbaka, suke tinkaho da karfin tattalin arziki, to komai yanzu zai zo karshe, saboda wadannan al’ummu biyu sun koma sun dinke, sun koma karkashin wani shugaba guda daya shi ne Annabi (ﷺ), kuma karkashin addini guda daya shi ne addinin Musulunci.
4. Wannan ya sa Yahudawa suka yi ta neman duk wata dama da za su yi amfani da ita don su ga sun dawo da wannan fitinar cikin wadannan kabilun guda biyu.
5. Wata rana mutanen Ausu da Khazraju suna zaune, sai wani bayahude da ake kira da Shas Ibn Kais shi da mabiyansa suka zo wurin suna karanta wakokin da Larabawan nan suka rika yi na nuna bajinta da zuga ga kabilunsu lokacin da ana gwabza yaki a shekarun da suka wuce. Saboda haka sai wannan ya tayar da ciwon dake cikin zukata wanda ya kusa ya warke ko ma ya warke sanadiyar zuwan Musulunci.
6. Saboda haka da jin haka sai kowa ya ta shi yana neman agaji daga dan’uwansa, kowa ya ja daga, aka zare takubba da masu, kowa na neman afkawa dan’uwansa. Ana haka sai labari ya iskewa Annabi (ﷺ) cewa ga halin da ake ciki tsakanin mutanen Ausu da Khazraj, sai Annabi (ﷺ) ya je wurin cikin gaggawa, ya tuna musu ‘yan’uwantakar da take tsakaninsu ta Musulunci, ya yi musu wa’azi, nan da nan suka zubar da makamansu suka rungumi junansu. [Duba, Ibn Hisham, Juzu'i na 2, shafi na 418].
7. To daga nan ne Allah (() ya sake saukar da wannan ayar yana jan hankalinsu cewa kada su yarda su ba wa Yahudawa wata dama, idan kuma suka yi haka, to Yahudawa ba za su kyale su ba, za su mayar da su irin rayuwarsu ta da, ta arnanci, ya zamana ba su san komai ba dangane da abin da ya shafi zaman lafiya. Daga nan Allah ya saukar da aya ta 100 zuwa 101 ta Suratul Ali- Imaran.


https://t.me/miftahul_ilmi
Post a Comment (0)