KADA KA GAJIYA...



KADA KA GAJIYA... 

Duk sadda zuciyarka tayi raunin da take raya maka cewa : *"Tun yaushe kake ta yin addu'a, amma har yanzu baka ga amsa ba"*

Toh ka sani shaidan ne ya d'ana maka babban tarkonsa wanda zai iya gangarawa da kai cikin halaka mai girma. Don haka kayi maza ka ya'ke shi, ta hanyar neman tsarin Allah daga sharrinsa, sa'anan ka kara jaddadawa zuciyarka cewa: *"Bautar Allah kake yi da yin wannan addu'ar, domin Manzon Allah (SAW) yace Addu'a ibada ce. Don haka duk sadda kayi toh lada kake samu. Kuma wanda ma baya roqon Allah toh Allahn zaiyi fushi dashi. Saboda haka sai ka kara kaskantar da kanka a gaban Wadataccen da ba'a ta6a wadatuwa daga gareShi.*

A wasu lokutun kuma an kar6i addu'ar, saide akan jinkirtawa bawa ne zuwa wani lokaci na musamman koh a bashi wani abunda yafi wannan mahimmanci da alkhairi ga rayuwarsa, koh anyi masa tanadin wani matsayi mai girma acikin Aljannah a dalilin naciya da juriyarsa wajan yin addu'ar (duk da buqatar tasa bata biya ba).

Ya ishi mutum samun natsuwa da farin ciki ace ta dalilin roqon Allah da yake yi ana bashi lada.

Ku sani ya ku 'yan uwa masu albarka; kunga rashin cikakken yaqini, rashin bin matakai da shari'a ta shiryar wajan yin addu'a, gaggawa, cin haram da aikata zunubai sune manya manyan shamakan da suke hana a amsa addu'ar bawa.

# Zaurenfisabilillah

Telegram:
https://t.me/Fisabilillaaah

Instagram:
https://www.instagram.com/zaurenfisabilillah/
Post a Comment (0)