TSAKANIN MU DUK DA BANBANCINMU 23


*⚖️TSAKANIMMU DUK DA BAMBANCIMMU//23📿*

*GINSHIQI NA 21*

*Rubutawa: Baban Manar Alqasim*

GUJE WA CAKUDA HUKUNCI DA DABI'A TA HALITTA

Dan adam a halayensa da dabi'unsa yakan bambanta da wani, kamar yadda wani gari kan bambanta da wani, wani nan-da-nan sai ka ga ya zuciya a kan dan qaramin abu, wani kuwa sai a yi ta yi ba tare da ya damu ba, irin mai saurin hawannan in ya zo ma'amalla da fandararre sai ka ga ya tsananta matuqa, tare da nuna cewa hakan fa shi ne abinda addini yake buqata wurin nuna qauna ko qiyayya a addinance, a dalilin hakan sai ya fara nemo dalilan da suka dace da dabi'arsa don kafa hujja -a zahiri ba haka shari'a ta gindaya ba- sai ya dage sai ya qwaqulo abinda zai qarfafa matsayinsa.

Wani kuma ya cika sanyi matuqa, sai a yi ta keta iyakokin Allah SW da shar'o'insa yana kallo amma ya ja bakinsa ya tsuke, ya gaza kawo hujjojin da zai ba da kariya a kai, a haka har a yi wa addinin Allah rauni, to ita shari'ar Allah matsakaiciya ce, ba wannan ba wancan, musulmi kan kiyaye ayyukansa ne da kai-komonsa daidai da addini, in zai fushi da wani to a tsukin inda aka iyakance masa ne.

In addini ya yi wa musulmi umurni da ya yi fushi yakan nuna fushinsa, inda ya umurce shi da karbar abu kuma yakan amince ya karba, inda aka ce ya yi tsanani yakan yi, inda aka buqaci ya sassauta yakan sassauta, tsanantawa kan kasance ne tare da kafurai a yayin dauki ba dadi, kamar yadda Allah SW ya ce ((Annabi ka yaqi kafurai da munafuqai ka tsaurara musu, makomarsu jahannama ce tir da wannan makomar)) At-Tauba 73. Kenan akwai buqatar fiqihun yadda za a yi ma'amalla da wanda ba kafuri ba ba kuma munafuqi ba.

Dangane da muslmai ya ce ((Muhammad manzon Allah ne, wadanda ke tare da shi sukan matsa wa kafurai su tausaya a tsakaninsu, za ka gansu cikin ruku'i da sujjada suna neman falalar Allah da amincewarsa, akwai alamunsu a goshinansu na yin sujada, wannan shi ne misalinsu a At-Taura, a Injila kuwa kamar tsiro ne da ya fidda ganyensa, [ganyen] ya qarfafa shi, ya yi kauri, ya tsaya qyam a tushensa, yana ba wa manoman sha'awa, [wannan wato kamanta yawan sahabbai da qarfafa Annabi SAW] don ya je fa damuwa ne a zuciyar kafurai, Allah ya yi wa wadanda suka yi imani da aiki na qwarai alqawarin gafara da lada mai girma)) Al-Fath 29.

Ibn Taimiyya yake cewa a cikin mutane za ka sami wanda yake da dabi'ar sanyi, taushi na qarshe da qauna, sai ya yi aiki da qaunarsa, girmamawarsa, amfanarwarsa da dukiyarsa ga abubuwa masu kyau wadanda Allah SW yake so, kuma ya yi umurni da shi, kamar son Allah da manzonsa, da salihai na qwarai dake zagaye da shi, da ciyarwa saboda Allah da sauransu, duk da haka kuma yana son alfahasha, yakan ba da dukiya don yinta, sai ka ga yana son gaskiya da qarya a gwamatse, ya yarda da su gaba daya yana taimaka wa duk wanda ya taso.

"Daga cikinsu kuma za ka taras da tsayayye, wanda yake nisantar alfahasha, yake qinta, amma duk da haka bai son taimakon mutane, bai kyautata musu, ba kawaici in sun munana masa, sai ka taras yana qin gaskiya da barna a gwamatse, duk ya qaryata su gaba daya, bai taimakon dayansu sai ma ya toshe su gaba daya (Qa'idatun fil mahabba 1/135), na farko sanyinsa da taushinsa sun bata masa ma'aunin da zai iya rabe daidai da kuskure, ya rabe alkhairi da sharri, sai wannan sanyin ya sa ya karbe su gaba daya kawai, tare da zaton cewa hakan ne daidai, zai iya daukar kuskuren ya ma taimaka masa, duk wanda ya bi shi ko ya yi kuskure sai ya kau da kansa duk barnarsa, matsalar da 'yan dadi arna suka sami kansu kenan a ciki da 'yan boko zalla masu son magana a kan addini.

Na biyu kuwa tsananinsa ne ya sa ya matsa wa mutane gaba dayansu, na gari da mutanen banza, bai girmama na gari bai daga wa mai kuskure qafa, duk wanda ya saba masa ya shiga uku, ya dora kuma cewa duk wannan neman kusanta ce ga Allah SW, wannan kuma matasammu ne a ciki 'yan kowa malam, karatun bai yi yawa ba amma suna ganin daidai suke da malamansu ko ma fiye, in aka kira sunan wani malami sai ka ji sun ce "Au wannan dan bidi'a ne kar ka yi karatu a wurinsa" addini koyaushe matsakaici ne.

Zamuci gaba insha Allah.

*Gabatarwa: Abulfawzhaan*

*Follow my Facebook Page*
https://www.facebook.com/100625758324355?referrer=whatsapp
Post a Comment (0)