KARIYA DAGA MAI HASSADA

*_KARIYA DAGA MAI HASSADA!!!_*

                                 *Tambaya :*
Assalamu alaikum Akaramakallah, ina da wani aboki na  kud-da-kud, saidai ba ya so ya ga na fi shi da wani abu, idan na samu wani abin alkairi, sai ya aibanta abin ta yadda mutane ba za su kimanta shi ba, abin yana damuna, shi ne na ke so a taimaka min da hanyoyin da zan samu kariya daga mahassada ?

                                     *Amsa:*
Wa'alaikum assalamu, To dan'uwa ya kamata ka san cewa babu yadda za ka yi ka wofantu daga mahassada, domin duk wanda Allah ya yi masa ni'ima, dole sai ya samu mahassada, saidai duk da haka akwai hanyoyin da malamai suka fada, wadanda suke hana hassadar yin tasiri

1. Neman tsari a wajan Allah daga sharrinsa.

2. Tsoron Allah da kiyaye umarninsa, duk wanda ya kiyaye Allah, to zai kiyaye shi.

3. Yin hakuri akan abokin gabansa, kar ya ce zai rama mummunan abin da ya yi masa, domin in har bai rama abin da aka yi masa ba, to tabbas Allah zai rama masa.

4. Karfin dogaro zuwa ga Allah, Allah  yana cewa a cikin suratu Addalak aya ta 3 "Duk wanda ya dogara ga Allah, to ya ishe shi" idan ka dogara ga Allah sharrin mahassadi ba zai cutar da kai ba, ko da kuwa ka ga wani abu da yake na cutarwa ne to karshensa zai zama alkairi.

5. Fuskantar Allah madaukaki sarki da tsarkake aiki zuwa gare shi, da yawan ambatonsa.

6. Tuba daga zunubai, domin ba za'a dora maka wani ya dinga cutar da kai ba, sai idan akwai wani zunubi da ka aikata, ka san zunubin ko ba ka san shi ba.

7. Yin sadaka da kyautatawa iya abin da zai iya, saboda da wuya Allah ya dora mai hassada akan wanda yake kyautatawa mutane.

8. Kyautatawa wanda yake yi maka hassadar, saidai wannan yana da tsananin wahala.

In har ka kiyaye wadannan Allah zai taimaka maka, don neman karin bayani duba Bada'iul fawa'id 2\463.

Allah ne ma fi sani.

1/4/2014

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)