MECECE RIBA?

*​MENENE RIBA?*

*Tambaya:*

 

Assalamu alaikum
 Don Allah Malam Menene RIBA a musulunci?

*Amsa:*

Wa alaikum assalam To malama riba ta kasu kashi biyu :
*1.* Akwai ribar jinkiri, kamar ka ba mutum bashin naira hamsin, ka nemi ya dawo maka da naira sittin, ko kuma idan ka bawa mutum bashi, ya yi jinkirin biya, ka ninninka masa kudin da ka ba shi, irin ribar da ake amsa a banki, za ta shiga cikin wannan bangaren.
*2.* Ribar fi-fiko, kamar yanzu, ki bada naira 1100 tsofafi, a ba ki naira 1000 sababbi, ko kuma ki bayar da shinkafa 'yar gwamnati kwano uku, a ba ki shinkafa ta gida kwano hudu.

Duka wadannan nau'oin guda biyu Allah ya haramta su, kuma ya kwashe musu albarka.
Allah shi ne mafi sani
*Amsawa*✍🏻
*DR. JAMILU YUSUF
ZAREWA*

23/4/2018

1 Comments

Post a Comment