TAMBAYA AKAN HAILA



*TAMBAYA*❓

Assalamu alaikum malam akwai wasu lokuta wadanda idan HAILA ta zowa mace bata yi salloli ba to ya za ayi ? Ko kuma idan jinin ya dauke mata a wannan hali to yaya zatayi ? Ma'ana Wacce Sallah zata rama kuma wacce ce bazata ramaba?.

*AMSA*👇


1. Idan mace mai jinin Haila ta samu tsarki (jini ya dauke mata tai wanka) . Hailarta ta dauke da yamma Sauran Minti 20 Rana ta fadi ..sai ta sami tsarki a wannan lokacin to za ta Rama sallar Azhar Da la'asar.....idan kuma bai kai misalin minti 20 ba kamar idan saura minti 18 rana ta fadi to wannan lokacin zata rama Sallar la'asar kawai ba zata rama sallar Azhur ba
2. Idan mai jini Haila ta samu tsarki (ma'ana hailarta ta dauke tai wanka) Amma wannan lokacin ya kasance da daddare ne ..Saura miniti 17 Alfijir ya hudo, to sai tayi Sallar magariba da isha'i .Amma idan bai kai minti 17 ba .kamar idan saura minti 15 Alfijir ya hudo to za tayi sallar isha'i amma bazata rama magrib ba
3. Idan mace batai sallar Azhur da la'asar ba ,sai jinin Haila yazo mata to yaya zatayi ? Sai ta duba ta gani idan saura minti 17 rana ta fadi to wannan idan jini ya dauke mata zata Rama Sallar Azhur bazata rama la'asar ba ..Domin jinin Haila yazo mata ne a cikin lokacin sallar La,'asar shine yasa ba zata rama Sallar la'asar ba
4 idan mace ba ta yi Sallar magrib da isha'i ba sai jinin Haila yazo mata to yaya za ta yi? ..Zatayi la'akari da gwargwadon mintina idan za a sami Sauran miniti 13 alfijir ya keto (ya fito) to anan za ai sallar magrib kawai banda isha'i domin jinin hailar yazo mata cikin lokacin isha'i tunda Alfijir bai keto ba shine yasa bazata rama Sallar isha'i ba idan ta samu tsarki .....
Note
Idan mace jini ya dauke mata kafin fitowar Alfijir idan lokacin ramadana ne wannan azumin na ranar dole ayi shi koda batai wanka ba..da safe sai tai wankan ...Haka kuma da za ta kwanta ta wayi gari da safe sai ta duba bata ga jini ba ..Kuma ba ta da tabbacin lokacin da jinin nan ya dauke Dole ta kame bakinta bazataci ko tasha ba har sai ansha ruwa Bayan sallah kuma ta rama wannan azumin idan kwa taci tash to zatai azumi guda 60 domin tayi ganganci da Azmi ...Allah ya sa mu dace .....
Wannan shi ne dangane da wannan bayani ga duk wacce take so ta samu wannan abu mai mahimmanci ga kowace ya mace domin ba a bautawa Allah da rashin sani..kula da wannan abun shi yake nuna mana sallar mu tana karbuwa...domin idan ba a san wannan ba to za a dinga Barin wasu sallollin idan jinin yazo ko idan ya dauke domin ba a san yadda za ai ba.

Allah yasa mu dace ameen.
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)