MATA A FINA-FINAN INDIYA 01



💎🍁💎🍁💎🍁💎🍁💎🍁💎🍁
MUJALLAR FINA-FINAN INDIYA 
💎🍁💎🍁💎🍁💎🍁💎🍁💎🍁

KE GABATAR MUKU DA SHIRIN


༄🌼༄🌼❄️✿🌀...♡...🌼༄🌼༄
MATA A FINA-FINAN INDIYA
༄🌼༄🌼❄️✿🌀...♡...🌼༄🌼༄

                 Kashi na (01)

                   Tare da

            •----------•✬(✪)✬•----------•
                   Haiman Raees 
           •----------•✬(✪)✬•----------•


            •┈┈••♡🍃♡••┈┈•
              12th July 2021 
            •┈┈••♡🍃♡••┈┈•



Wannan wani sabon shiri ne wanda hukumar wannan gida ta ƙirƙiro domin ya dinga zaƙulo muhimman abubuwan da suka shafi mata a masana'antar shirya fina-finan Indiya baki ɗaya. Muna fata za ku karɓe shi hannu biyu. 


A Faro daga tushe. 


A tsakanin al'umma irin na ƙasar Indiya, akwai irin yanayin da ake so mace ta fito a cikinsa yayin ɗaukar fim domin ya dace da waɗannan al'umma. 
Misali, mace ta fito a matsayin Sita a fim. Sita ɗaya ce daga cikin jaruman labarin Ramayana, ɗaya daga cikin labaru mafi shahara a ƙasar Indiya waɗanda ke ƙunshe da ladubba tare da nuna banbancin da ke tsakanin daidai da rashin daidai. Sita mata ce ga Rama wanda aka ce yana bayyana zubin abubu nagari kamar daraja, jarumta, da kuma amana. Mafi yawancin fina-finan Indiya sun samo asali ne daga ɓuɓɓugin labaran Ramayana da kuma Mahabarata wanda ya ƙunshi labarin abin bauta Krishna. Sita nagartacciyar mace ce wacce ta ke ganin mijinta da ƙima kuma shi ne abin koyi a gare ta. Wannan dalili ya sa fina-finan farko-farko na Bollywood suke nuno mata da siffa irin nata domin ya dace da al'ummar yankin su. 

Haka kuma, a cikin wani gagarumin aikin mai taken Manusmriti, wani kundi ne wanda yake magana akan shari'o'i, ɗa'a da kuma tarbiyya. A cikin sa, an bayyana cewa wajibi ne mace ta miƙa wuya wa Mahaifinta yayin da take ƙarama, a yayin da ta girma kuma wa mijinta, bayan ta tsufa kuma ko in mijinta ya mutu, to ta maida hankalinta kacokan wa 'ya'yanta. 
  
Kamar yadda aka tsara a cikin Manusmriti, mata ba su san daɗin 'yanci ba. A kullum abin da ake buƙata daga mace kawai shi ne kullum ta fito cikin farin ciki kuma ta kasance cikin kula da gidan ta. Kullum so ake ta kasance me biyayya ga mijinta, har bayan ransa. 

Ko da yake masana'antar fina-finan Indiya tana canjawa tare da samun ci gaba, matan da ke fitowa a cikin irin wannan siga sau da dama ana nuna su da cewa suna cikin farinciki kuma suna da ɗa'a matuƙa. Waɗanda kuwa ba sa fitowa a irin haka ko suke sukar hakan, ana ganin cewa basu da ɗa'a kuma ya kamata a hukunta su. 

Irin wannan yanayi ko siga, shi ne mafi shahara daga cikin irin sigogin da mata ke fitowa a cikin sa a fina-finan Indiya. 

Amma a yanzu, ana iya raba irin sigogin da mata ke fitowa a cikin fina-finan Indiya zuwa gida huɗu kamar haka:

Siga farko: Matar Aure

Wannan ita ce sigar nagartacciyar mace wacce babu ruwanta da baɗala da duk wani nau'i na rashin ɗa'a. Ya zama wajibi a kanta ta tsaya tsayin daka wajen ganin ta martaba al'adar indiyawa kuma dole ta ɗaukaka darajar gidanta ta hanyar kulawa da shi, kuma dole ne ya zamana ta dogara da mijinta ba wani ba, ba kuma kanta ba. Kuma wajibi ta kasance me zage damtse wajen aikace-aikacen gida 


Siga ta biyu: Mahaifiya

Ita wannan an fi jingina ta da abubuwan da suka shafi addini, don haka ba a taɓa samun ta da yin abin da be dace ba. Indiyawa da yawa suna ɗaukar Mahaifiya da matsayi irin na abar bauta. Wannan kuma ya samo asali ne saboda alaƙar da suke da shi abar bauta Shakti wacce take da ƙarfin gaske a tsakanin addinai da kuma al'adun su. Wannan dalili ya sa har yau indiyawa suke ba wa Mahaifiya matsayi na musamman a cikin fina-finan su. In kana son ganin irin yadda ake nuna girman darajar uwa sosai, kana iya kallon Mother India (1957), a kwana kwanan nan kuma kana iya kallon KGF: Chapter 1 (2018)

 Siga ta uku: 'Yar ƙwalisa 

Wannan ita ce 'yar zamani, kuma tana koyon duk wata ɗabi'a irin ta turawan yamma. Daga cikin halayenta akwai shan ƙwayoyi, busa sigari, shan giya, tiƙar rawa a kan titi da shiga ta fitsara sannan tana iya faɗawa soyayya kuma ta fita kafin ka ƙyafta ido. A koda yaushe irin wannan takan samu hukuncin da ya dace da ita. 



 Siga ta huɗu: 'Yar balaja'u

Ita kam irin wannan, ta shallake duk wani mataki na rashin ɗa'a a bisa al'ada irin ta mutanen Indiya, ta ma koma tamkar wata karuwa ko kuma 'yar casu kawai. A koda yaushe ita kawai nuna tsiraici ne aikin ta tare da jan hankalin maza zuwa gare ta. Kai ana sa irin wannan a fim ne ma kawai domin ta kashe ƙwarƙwatar idanuwan mazaje ba don lale ta iya aiki ba, ba kuma don ta isar da wani muhimmin saƙo ba. A ƙarshe akan nuna irin waɗannan mata sun rasa wanda suke so ɗin kuma sun ƙare cikin takaici ko kuma su yi mutuwar wulaƙanci. 

A taƙaice, waɗannan su ne ire-iren sigogin sau da dama mata ke fitowa a ciki a masana'antar fina-finan Indiya. To yau da gobe ana samun canje-canje da kuma ƙalubale iri-iri. Amma kafin mu je can, za mu ci gaba da tattauna batun mu da muka fara na a fara daga tushe. 

Ku tare ni a shiri na gaba don jin abin da ke gaba. 


©️✍🏻
  Haiman Raees 
# haimanraees 
Haimanraees@gmail.com

Miyan Bhai Ki Daring
Post a Comment (0)