TA MANTA BATAYI WANKAN JANABA BA



*TA MANTA BATAYI WANKAN JANABA BA.*

      *TAMBAYA*❓

Assalamu Alaikum
Malam mace ce take haila sai sha'awa ya kamata har maniyyi ya fito amma Tana cikin kwanakin hailarta bayan ta gama hailar sai tayi wankar haila kawai Tama manta da cewar maniyyi ya fito mata alokacin da take haila ta sanadiyar sha'awa toh sai yanzu kwatsam sai ta tuna toh malam shin wanka ya wajaba akanta ne domin fitar wannan maniyyin ko kuwa, sannan Kuma idan har zatayi wanka sbd fitar maniyyin gashi Kuma ta Riga da tayi wankan haila kawai shin malam ya zatayi yanzu?
.
         *AMSA*👇🏻

wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuhu


Na.am da hailar da janabar duk manyan karine, duk bayanai sun gabata sosai akan wannan mas'alar zamu kuma maimaitawa
.
da ace lokacin da janabar tasametane saitayi wankan janabar domin rabuwa da janabar badon tayi ibadaba, duk da akwai malaman dasuke da ra'ayi saɓanin hakan kamar yanda bayanai suka gabata, ita wannan data tuna cewa akwai janaba ajikinta bayan ta daɗe da samun tsarki kuma tayin wankan hailarta, toko shakka babu ana binta bashin wankan janaba, dan haka yayin data tuna saitaje tayi wankan janabar.
.
da ace lokacin dazatayi wankan hailar ta tuna cewa tanada janaba dasaita haɗa wankan janabar dana hailan tayi niyya biyu awanka ɗaya ya wadatar insha Allah.

Wallahu a'alam.

(( ﺳُﺒْﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ، ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥْ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ، ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ))
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)