TSOHUWA DA DAN ACABA



TSOHUWA DA DAN ACABA
Wata tsohuwace tahau mashin din wani dan achaba zai kaita unguwa. Inda zai kaita naira arba’in ne a ke kaiwa tace yataimaka naira ashirin ne gareta yace tahau bakomi. Ke tsohuwa dakika hau mashin kikaji anata tsula wuta dake saita rasa inda zata rike dan karta fado kawai taji wasu marikai guda biyu daga kasa ashe siginoni ne tsohuwarnanko tarikesu gamgam da taji an kara shiga gargada garam!Garam! Saita kara makalkale siginonin nan daga karshe dai kamin akaita inda zata sauka duk ta kakkarya siginonin mashin dinnan sai da dan achabar nan yakaita bayanta bashi ashirin din saita mika mishi siginonin tace karbi yaro abubuwan rikewar taka basuda kwari!!! Dan achabarnan yayi shiru yana kallon tsohuwarnan. Yarasa abinda zaiyimata yahuce karshe yace to dan allah iya taimaka ki rike minsu muje wajan me mashin din karya ce dagangan na karyasu sai kiyi masa bayani. Tsohuwa tace bakomi da yadauketa yayita zuba gudu saida yayi tafiyarda ko naira dari da hamsin bazata maida tsohuwar nan ba sannan ya tsaya yaceta sauka bayan tasauka yakalleta yace yar banza kudin siginata yaja mashindinshi yatafi yabar tsohuwanan tsohuwa tafashe dakuka tace Allah ya isa, yaro kwarankwatsa naira goma taragemin.
Post a Comment (0)