WACE CE RUMAISA (UMMU SULEIM)? 00



WACE CE RUMAISA (UMMU SULEIM)
  
                        ❓
          
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

             GABATARWA

   Duk kan yabo da godiya sun tabbata ga ubangijin al'arshi tsira da amincin su tabbata ga farin jakada babba dan Abdullah Muhammadur rasulullah saw da iyalansa da sahabbansa da da wadanda suka biyo bayansa har izuwa ranar qarshe. 

Bayan haka wannan wani dan taqaiceccen littafi ne da muka rubuta bisa tarihin daya daga cikin mata manya "yan gaban farin jakada babba dan Abdullah Muhammadur rasulullah saw wanda tarihin mata sahabbai bazai cika ba ba tare da ita ba wato 🌹RUMAISA🌹 wanda bazamu tsawaita ba wajan rubuta tarihin wannan baiwar Allah zamu taqaita rubutun domin kada mu gajiyar da mai karatu zamu taqaitu akan littattafai guda hudu wajan kawo ingantaccen tarihin ta sune kamar haka :
1- سير أعلام النبلاء
2- النساء حول الرسول
3- نساء أهل الجنة
4- مؤمنة الصادقة

Wadannan sune madogararmu wajan bibiyan tarin wannan baiwar Allah Abubuwan da zamuyi magana dan gane da ita sune kamar haka :

1- sunanta da nasabarta
2- Mazajen da ta aura
3- Sadakinta ga Abu dalha
4-"Yayanta
5- Qissar mutuwar dan ta
6- Addu'ar manzan Allah ga Anas
7- Addu'ar manzan Allah ga abincin gidanta
8-Kyautarta ga manza Allah saw
9- Neman tabarrakinta da manzan Allah
10- Jarumtakarta
11- Darajojinta
12- Dalibanta
13- Bishararta ga Aljannah
14- Mutuwarta
15- manufar wannan rubutun

Wadannan sune abubuwan da zamu taqaitu akansu wanda in sha Allah zamu kawo muku shi batare da tsayawa ba saboda mahimmancin wannan rubutun yasa muka dakatar da duk kan rubuce-rubucenmu har sai mun kammala wannan rubutu. 

Muna kira da malumammu da "yan uwammu daliban ilimi akan cewa duk inda aka ga munyi ba dai ba ayi saurin riskar damu kamar yadda aka saba domin muma muyi sauri wajan riskarsa kafin ya yi nisa muna roqan ubangijin al'arshi akan ya bamu damar rubuta dai dai ya nisantar damu daga kuskure yasa munayi ne domin neman yar dar sa Ameen ya hayyu ya qayyum.

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

MU HADU A FUTOWA TA 01

Rubutawa... ✍️✍️✍️✍️✍️
         Dalibi mai neman ilimi Nazifi Yakubu Abubakar
             (Abu Rumaisa)
          🥏08145437040🥏
Post a Comment (0)