BAMBANCI {18}
Kada ko kusa damuwa ko tsananin jin zafin ciwo yasanya ki kirika zuwa karbar magani wajan mutanen nan kamar haka:
1- Yan bori.
2- Bokaye masu yanayin gargajiya ko kuma na zamani.
3- Waɗanda aljanu suka mayar da su masu bayar da magani... Da sauarsan.
Masu zuwa irin wuraren nan su ne za kuga kullum cikin damuwa da rashin samun saukin cututtukan su, hasali ma aljanun kara samun mazauni suke yi ajikin su kuma su karu, ko da ma an samu saukin to na wasu yan lokuta ne sai matsalar ta dawo kuma ba a cika rabuwa da irin matsalar ba saboda an qulla alaka da shedanun nan kuma a gaba a hadu da fushin Allah, Saboda Shari'ar ALLAH ta haramta zuwa irin wuraren nan.
Amma idan mutum yatsaya yin magungunan cutarsa ko matsalarsa da abinda Allah da Manzon Sa (Sallallahu alaihi Wasallama) suka halalta kuma suka yarda da hanyar aikatawa kaɗai, to tabbas ba makawa shi ya more kuma ba makawa sai Allah ya jibinci lamarinsa.
Daga cikin abinda mutum zai yi amfani da su wajan magance matsalar Jinnul Aashiq akwai na Alqur'ani da ake tofawa a ruwa kuma a rika shansu, akwai kuma na wasu ciyawu ko itatuwa waɗanda suke halal ne a musulunci. Ga na Alqur'ani nan kamar haka:
Shi Alqur'ani gaba dayansa waraka ne kuma magani ne, duk Ayar da mutum ya karanta insha ALLAHu matuƙar ya nufaci Allah kuma zuciyarsa a tsarkake take wajan baiwa Allah cancantarSA, to ba makawa Allah zai taimake shi kuma yajibinci lamarinsa, amma akwai wasu Ayoyi da Surorin da malamai suka kebe su sukayi bayaninsu kamar haka :
1- Suratul Fatiha
2- Ayoyi biyar na farkon suratul Baqara
3- Ayatul Kursiyyu
4- Ayoyi 2 na Karshen Suratul Baqara.
5- Ayoyin da sukayi magana akan sihiri dake cikin Suratul A'araaf (daga 106 -122), Suratu Yunus (Daga 78 - 82), Suratu Taha (Daga 65 - 69) .
6- Suratul Kafirun, Ikhlasi, Falaqi da kuma Naasi.
7- Da kuma wasu Addu'o'in da suka zo a cikin Hadisan Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama.
A rubutu nagaba insha ALLAHu za mu fadi yadda yakamata ayi da waɗanda Ayoyin da ma wasun su..
Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.
Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.
(Ayi mana Addu'ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu.🤲🏻)
Domin karin bayani:
👇👇👇
Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu'aym)
Gmail:
rismawy86@gmail.com
WhatsApp :
+2348031542026
Telegram Channel:
https://t.me/Rismawymedicine