WACE CE RUMAISA (UMMU SULEIM)? 01


WACECE RUMAISA (UMMU SULEIM)
  
                             ❓

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

FUTOWA TA 👇
            (01)


SUNANTA DA NASABARTA

   Idan aka ce 🌹RUMAISA🌹 a larabci yana daukar ma'anoni da yawa daga cikin ma'anonin yana daukar Abu wanda yake (madaukaki sosai ko kuma wayayyen mutum). 

Ummu suleim tana daga cikin mata sahabbai wadanda suka shahara da Alkunyarsu sama da sunayen su, An samu sabani wajan malamai akan Haqiqanin sunanta aqalla magana guda 10 wasu suka ce, 🌹Gumaisa'u wasu suka ce Rumaisa'u wasu kuma suka ce Sahla wasu suka ce Rumailah wasu suka ce Unaifah wasu kuma suka ce Rumaitha wasu kuma suka ce Mulaika wasu kuma suka ce Ramla wasu kuma suka ce Unaisa wasu kuma suka ce Uthainah🌹 wadannan sune sunaye guda Goma 10 da aka samu sabani dan gane da ita, ibn Hajar yace GUMAISA'U suna ne nata RUMAISA'U kuma suna ne na "yar uwarta amma abun da yafi tabbata shine abun da ibn Abdulbar ya fada yace duk biyun sunayenta ne Amma abun da yafi shahara abakin mutane shine 🌹RUMAISA🌹. 

Sunan mahaifinta Milhan dan Khalid dan Zaid dan Haram dan Jundub dan Amir dan Ganam dan Adiy dan Najjar Mutuniyar garin Madina kuma "yar Qabilar kazrajiyyah. 

Babu wani abu da aka rawaito dan gane da mahaifinta sai dai abun da aka rawaito acikin littafin Al'ISABAH ta ibn hajar cewa manzan Allah saw yana cewa "An kashe babanta da dan uwanta tare da ni". 

Mahaifiyarta kuma sunanta Mulaika ko Unaiqah "yar Malik dan Adiy dan Amru dan malik dan Najjar ta riski musulunci kuma ta musulunta. 

Tana da "yan uwa mata da maza, mazan su Hiram da Suleim sun halacci yaqin Badar da Uhud da yaqin bi'iri kuma awannan yaqin sukai shahada su biyun duka. Mata kuwa sune Ummu hiram matar sahabi Ubada bn samit itama ta rasu a yaqin Qabris Sanadiyyar fadowa da tayi daga kan abun hawanta ta karya wuya a lokacin halifancin Usman bn Affan, ibn sa'ad ya kawo wata "yar uwar ta mai suna Ummu Abdullah bnt Milhan Kuma yace ta musulunta kuma tayiwa farin jakada babba dan Abdullahi Muhammadurrasulullah saw mubaya'ah Amma bai kawo wata bayan ta ba.


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

MU HADU A FUTOWA TA 02

Rubutawa... ✍️✍️✍️✍️✍️
         Dalibi mai neman ilimi Nazifi Yakubu Abubakar
             (Abu Rumaisa)
          🥏08145437040🥏
Post a Comment (0)