WACE CE RUMAISA (UMMU SULEIM)? 02 & 03

WACE CE RUMAISA (UMMU SULEIM)
  
                             ❓

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

FUTOWA TA 👇
        (2), (3)


MAZAJEN DA TA AURA DA KUMA SADAKINTA


     Ummu Suleim ta auri mazaje guda biyu na farkon shine Malik bn Nadar mahaifin Anas alokacin jahiliyya kafin zuwan musulunci ya yin da musulunci yazo garin madina tayi gaggawa wajan karbarsa tare da wadanda suka karbesa tun wuri ta sabawa mijinta, tun a wannan lokacin ta zama mai da'awa zuwa ga mahaliccinta domin ta kasance tana koyawa danta Anas kalimatush shahada tun yana qarami bai wuce shekara Hudu ba, sai tace ya kai Anas ce 🌹LA'ILAHA ILLALLAH🌹, mijinta kuwa Malik mahaifin Anas yana cewa ki daina koya masa wannan kalmar amma taqi yi masa biyayya, bayan haka yabar madina ya tafi Sham aka kashe shi akan hanyarsa wannan shine mijinta na farko. 

Mijinta na biyu kuwa ba kowa bane face Abu dalha Al'ansari lokacin da ya yi mata maganar Aure sai tace ya kai Aba dalha irin ka idan ya nemi aure ba'a mai dashi sai dai kai mutum ne kafiri ni kuma mace ce musulma baya halatta na aure ka.! 
    Sai yace da ita me kike buqata na baki ? Sai tace dashi me zaka bani na sadaki? Sai yace mata zinare da Azurfa! Sai tace Ni bana buqatar zinare da Azurfa, ina buqatar musulunci agurunka, idan ka musulunta wannan shine sadaki na bazan tambayeka wani abu ba bayansa ba. 
   Sai yace waye zai zama shaida akan haka sai tace manzan Allah (saw) sai Abu dalha ya tafi wajan manzan Allah (saw) a lokacin manzan Allah yana zaune cikin sahabbansa, ya yin da ya gansa sai yace "Abu dalha yazo wajanku hasken musulunci na tsakanin idanunsa" sai ya bawa Manzan Allah (saw) labarin abun da ummu suleim ta fada masa sai ya aure masa ita akan haka. 

Sabit Albunani yana cewa labarin sadaki mafi girma bai zo mana ba, saboda ita ta yadda musulunci ya zama sadakinta. 

An rawaito daga Anas yake cewa Aba dalha ya nemi auren ummu Suleim kafin ya musulunta, sai tace dashi shin ubangijin da kake bautawa ba daga qasa ya tsiroba, sai yace eh sai tace kuma baka jin kunya ka bautatawa bishiya, in dai zaka musulunta bana buqatar wani sadaki daga gareka , sai yace bari zanyi shawara sai ya tafi sannan ya dawo sai ya karbi kalmar shahada a take sai tace ya kai anas aura min Abu dalha. 

A ruwayar ibn sa'ad Anas yake cewa ya yin da Aba dalha ya nemi auran ummu suleim sai tace dashi nifa nayi imani da wannan mutumin kuma na shaida shi manzan Allah ne idan zaka bini akan haka zan aureka , sai yace nima nayi imani dashi, akan haka musulunci ya zama sadakinta da kuma cewa sai danta Anas ya girma ya fara zama, shi yasa yake cewa ubangiji ya sakawa Mahaifiyata haqiqa ta kyautata kulawarta agareni, saboda haka duk duniya ba'a samu wacce ta kaita Girman sadaki ba.



🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

MU HADU A FUTOWA TA 04

Rubutawa... ✍️✍️✍️✍️✍️
         Dalibi mai neman ilimi Nazifi Yakubu Abubakar
             (Abu Rumaisa)
          🥏08145437040🥏

Post a Comment (0)