ZANCE MAI CIKE DA HIKIMA



ZANCE MAI CIKE DA HIKIMA.

Idan ka shuka salak yau zaka girbe shi bayan sati uku, amma saidai ka cinye shi a ranar ko ya lalace.

Idan ka shuka shinkafa zaka girbeta bayan wata uku, kuma zaka iya ajiyeta har fiye da shekara biyu.

Idan ka shuka mangoro zaka fara tsinkarsa bayan shekara uku ne, amma duk shekara sai ka cika kwanduna ba tare da ka sake shukashi ba.

Idan ka shuka dabino, watakil ka tsinke shi bayan shekara goma sha uku. Amma hatta jikan ka sai ya tsinki É—ansa yaci, matukar ba sare shi akayi ba.

Ita duniya tana bukatar hangen nesa da hakuri, idan kayi shiri mai kyau kayi hakuri, Sai amfani mai dorewa yazo maka. Idan kayi mata gaggawa, Sai karamin amfani yazo maka.

Iya tsawon hakurin da Kayi, iya amfaninsa gareka, kuma hakane ake shiryawa ranar gobe kiyama;
*Kayi Aiki, Kayi Hakuri, Kayi Addu'a,.*

*Barkanmu Da War Haka.*
Post a Comment (0)