ASHE HAKA RUKU'U DA SUJUDA SUKE GOGE ZUNUBAI!



ASHE HAKA RUKU'U DA SUJUDA SUKE GOGE ZUNUBAI!

•Daga Jubair.. Ya ce lalle Abdullahi dan Umar yaga wani matashi yana Sallah, ya tsawaita sallar tashi, kuma ya dade a cikin ta, se Abdullahi ya ce, waye ya san wannan? Se wani mutum ya ce ni na sanshi, se Abdullahi ya ce; da ace ni nasan shi, da na ce masa ya tsawaita ruku'u da Sujuda, na ji Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi yana cewa; "Shifa bawa idan ya tashi yana sallah za'a zo da zunubansa gaba dayansu se a dora su a akanshi da kafadunshi, duk lokacin da ya yi 'ruku'u' ko 'sujuda' se su yi ta zuba.
.
 Sahih Albany da -Ibn Hibban
.
Note:
 Wannan hadisi yana Nuna mana falalan dadewa cikin ruku'u da Sujuda,Wanda zaka ga mafi yawan sallolin mu mun fi tsawaita tsayuwa.
To ga garabasa ga masu tsawaita ruku'u da sujuda.
.
Allah ta'ala ya gafarta mana.

TELEGRAM:
https://t.me/Fisabilillaaah

FACEBOOK:
https://www.facebook.com/Fisabilillaaah/
Post a Comment (0)