WAYE YAFI KUSA DA ANNABI MUSA ALAIHISSALAM, MU KO SU??
Ranar Ashura (goma ga watan muharram) ranace da Allah ya tseratar da Annabinsa Musa Alaihis Salam daga fir'auna da rundunarsa, hakan yasa Annabin Allah Musa yake azumtar wannan rana domin godiya ga Allah madaukakin sarki, suma yahudawa sai suke azumtar wannan rana domin koyi da Annabi Musa, Manzon mu kuma Annabi Muhammad sallallahu alaihi wa sallama shima sai ya fara azumtar wannan rana kuma yayi umarni da a azumceta, Sannan yace "Mu muka fi kusa da Annabi Musa sama da ku".
Sannan Ana so mutum ya azumci ranar tara ga watan, saboda wannan shine karshen umarnin Manzon Allah, kamar yadda yazo a hadisin Imam Muslim, idan kuma bai samu daman yin tara ga watan ba, zai iya yin sha daya ga wata, domin manufar yin tara ko goma sha dayan shine sabawa yahudawa da kuma kin kwaikwayonsu, wanda hakan dayane daga cikin manufofin musulunci.
Sannan falala mafi girma da daraja mafi daukaka shine mutum ya azumci kwani ukun gaba daya, ma'ana tara ga wata da goma ga wata da kuma sha daya ga wata, kamar yadda Shaikh Ibnu Uthaimeen Allah ya masa rahama ya fada.
TAMBIHI.
Mutane suji tsoron Allah su daina rudar da kansu suna rudar da jama'a, kullum malamai suna kokarin fadakar da mutane amma wasu ƴan social media kullum kara rudar da jama'a suke.
Yau litiniy 16/08/2021
lissafin mu na Nigeria 07/01/1442.
Tasu'a da Ashura zai zama ranar laraba da Alhamis ne in Sha Allah.
#Zurenfisabilillah
Telegram: https://t.me/Fisabilillaaah
Instagram:
https://www.instagram.com/zaurenfisabilillah/