BAMBANCI {21}


BAMBANCI {21}

Waɗan nan abubuwan da na lissafo a rubutu mai lamba ta 20, insha ALLAHu za muyi bayanin amfaninsu da ma wadansu da bamu lissafo su a baya ba ga mai shafar jinnu da kuma karfin da suke da shi wajen lalata sihirin da ke cikin jikin mutum da makamantansu.

HALTITI

Yana daya daga cikin abubuwan da suke takurawa jinnu kuma suna tasiri wajan kawar da sihirin da akaci a abinci ko wanda aka sha a abin sha ko ma dai wanne irin nau'in sihiri ne cikin yardar Allah. Yadda ake amfani da shi : 

1- Ana dibar garin haltiti gwargwadon gram 2, sai a sanya zuma cokali 2 da Habbatus saudah itama cokali 2, sai a sanya su a ruwan dumi kimanin kofi 1, sai a barshi tsawon mintuna 15, sai a rika sha safe da rana da daddare kullum sau 3.

2- Za a samu Haltiti wanda yakai yawan gram 3 ko 5 sai a samu man zaitun kofi 1, sai a zuba su a cikin wata kwalba a rufe sosai, sai a dora ruwa a wuta sai a sanya kwalbar da aka hada zaitun da Haltiti sai a barshi tsawon minti 30, sai a sauke shi kuma a bari ya huce sai a rika shafawa a jiki a duk dare, amma yakasance mutum ya yi alwala ne kafin ya shafa ya kwanta da Addu'a.

3- Ana zuba Haltiti ne gwargwadon gram 2 a cikin kowanne irin nau'in turaren hayaki ne, sai a rika turarawa mai fama da matsalar nan, Idan kuma zai iya yi da kansa sai yayi ba sai anyi masa ba.

Insha ALLAHu Allah zai bayar da waraka, wadanan kaɗan kenan daga cikin amfanin Haltiti ga wanda ya samu shafar Jinnul Aashiq ko kuma wanda aka yiwa sihiri.

A rubutu nagaba za muji Amfanin RAIHAN (Doddoya) wajan magance sihiri da shafar jinnu.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani. 

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu'ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu.🤲🏻)

Domin karin bayani:
👇👇👇

Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu'aym)

Gmail:
rismawy86@gmail.com

WhatsApp :
+2348031542026

Telegram Channel:
https://t.me/Rismawymedicine
Post a Comment (0)