BAMBANCI {22}


BAMBANCI {22}

RAIHAAN 

Da hausa shi ne : DODDOYA, yana daya daga cikin ganyen da suke da kamshi mai dadi kamar Na'a na'a, kuma ana yin magunguna da shi da dama ta hanyoyi mabanbanta, kamar yadda yarbawa da wasu kabilu suna yin miyar ganye (Vegetable soup) da shi, wasu kuma suna sanya shi a ruwan wanka ya jika zuwa wasu mintuna ta yadda za ayi wanka da shi domin sanya kamshin jiki.

A ɓangaren amfani da shi wajan magance Shafar Jinnu ko Kuma sihiri ana amfani da shi ne kamar haka:

1- A tsinko ganyen Raihaan (danye ko busasshe) sai a daka ko a nika shi sosai, sai arika dibar rabin cokali ana zubawa a cikin madara (mai dumi ko zafi) a kofi sai a rika sha sau daya kullum da daddare kafin a kwanta bacci har tsawon kwanaki 4.

2- Idan Sihiri ne sai a zuba garin Raihaan cokali 1 a kofi daya na madara (mai dumi ko zafi) sai arika sha da daddare kafin a kwanta har tsawon kwanaki 7 ko sama da haka.

ZA'AFARAAN

Ana shafa shi ne a jiki, yana matuƙar illata jinnu saboda suna matukar kyamar shi.

ALBASA

1- Albasa tana daya daga cikin abubuwan da Jinnu ke kyamar warin ta, shi yasa ana iya samun bawon albasar a hada shi da wasu abubuwan da ake yin hayaki da su, jinnu suna matuƙar kyamar warin hayaki.

2- Ganyen Albasa ko lawashi ana shanya shi ya bushe shi ma ana yin hayaki da shi,

TAFARNUWA

Itama tana daga cikin abubuwan da jinnu ba sa son warin ta kuma warin yana matuƙar damunsu kuma ya illata su, shi yasa masana suka ce ana sanya man tafarnuwa (amma mai kyau) a abinci ko a hada shi da sauran magungunan da aka hada domin magance matsalar jinnu da sihiri saboda yana da tasiri sosai wajan ruguza duk sammun da aka ajiye wa mutum a cikin ciki ko a jikinsa.

2- Kuma bawon tafarnuwa shi ma ana yin hayaki da shi ko a hada shi da bawon albasa da wasu abubuwan sai masu fama da jinnu ko sihiri su rikai amfani da su.

Insha ALLAHu a rubutu na gaba za mu ci gaba.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani. 

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu'ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu.🤲🏻)

Domin karin bayani:
👇👇👇

Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu'aym)

Gmail:
rismawy86@gmail.com

WhatsApp :
+2348031542026

Telegram Channel:
https://t.me/Rismawymedicine
Post a Comment (0)