HADISI YA HARAMTA MACE TA SA KAYAN MAZA, KO NAMIJI YA SA KAYAN MATA, TO YA HUKUNCIN MACEN DA KE SA KAYAN MIJINTA?



HADISI YA HARAMTA MACE TA SA KAYAN MAZA, KO NAMIJI YA SA KAYAN MATA, TO YA HUKUNCIN MACEN DA KE SA KAYAN MIJINTA?

*TAMBAYA*❓

ASSALAMU ALAIKUM, mlm barka da warhaka, mlm tambayata ita ce, mun karanta hadisai da suke nuna mana cewar ALLAH DA MANZONSA sun tsinewa namiji mai kamanceceniyyah da mata, haka ma ita ma macen, to mlm tambayata a nan ita ce shin mlm har da macen da ta sanya kayan mijinta don raha da wasa a tsakaninta da mijinta wanda kuma ba fita za ta yi da su ba?shin mlm ina hukuncin yin hakan?ALLAH yaqarawa mlm lafiya.

*AMSA*👇

Wa'alaikumus Salamu, Matuqar Shari'a ta haramta abu da nassi ingantacce kuma bayyananne, to ba ya halasta mutum ya ce zai kwatanta yin wannan abun don ya daɗaɗa ma wani, saboda haka ba ya halasta mace ta sa tufafin mijinta don wasa tsakaninta da shi, Ibn Abbas ya ce: Manzon Allah ﷺ ya la'anci masu kamanceceniya da mata daga cikin mazaje, da masu kamanceceniya da maza daga cikin mataye"
Bukhariy 5885.

A wani hadisin kuma da yake magana a kan sanya kayan ma quru-quru, wanda Abuhuraira ya ruwaito yana cewa: "Manzon Allah ﷺ ya tsine wa namiji mai sa kayan mata, da mace mai sa kayan maza"
Abu Dáwud 4098.

Saboda waɗannan dalilai, ba ya halasta namiji ya sa kayan mata ko na wace ce, haka nan ba ya halasta ita ma mace ta sa kayan maza ko na wane ne a zance mafi zama dai-dai.

Allah ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*✍🏻

SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)