HUKUNCIN SALLAR WANDA YA MANTA BAI YI KABBARAR HARAMA BA
*TAMBAYA*❓
Assalamu Alaikum Warahmatullaah
Malan inada tambaya... Ka tashi yin sallar azahar sai ka manta ba kayi kabbarar harama ba, ka fara karatu sai ka tuna, kawai ka mayar da ita Nafila, hakan ya halatta?
AMSA👇
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillah wa ala alihi wa sahbihi ajma'in.
Wanda ya yi nufin sallatar wata sallah ta wajibi, kamar ta Azahar, sai yana cikin sallar ya tuna bai yi kabbarar harama ba, da farko dai baya da wannan sallah. Na biyu kuma, ba zai halatta ba ya mayar da ita wannan sallar ta nafila ba, domin dukkan nau'in sallah kowace iri ce, bata inganta sai da kabbarar harama, saboda hadisin Annabi da yace
5885 - «مفتاح الصلاة الطهور وتحريمها التكبير وتحليلها التسليم» ... [حم د ت هـ] عن علي.
(صحيح) المشكاة 312، صحيح أبي داود 55، الإرواء 301، صفة الصلاة ص 66.
Wannan hadisi ya tabbatar da rashin ingancin sallar da aka bude ko aka gina ta ba tare da an yi kabbarar harama ba. Haka kuma ya tabbatar da cewa kowace sallah sai an zo mata da kabbarar harama.
Don haka abin da zai yi shine, sai ya zo da kabbarar harama ya fara wata sallah sabuwa ya jefar da duk abin da ya sallata ko ya aikata na karatu sujada, ruku'u da sauran aiyuka da zantuka.
Wallahu ta'aala a'lam.
Amsawa:
Malam Aliyu Abubakar Masanawa
Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177