HUKUNCIN SHAYARDA JARIRI RUWAN NONO ZALLAH TSAWON WATA SHIDDA.
TAMBAYA TA 00214
*******************
Assalamu alaikum. Dan Allah ina da tambaya shin exclusive breast feeding akwai shi a addini??
AMSA
***
Wa'alaikumus-Salam. Hakika A Cikin Al-qur'ani Mai Girma Suratul Baqara Allah (Saww) Yana Cewa, "Kuma masu haifuwa suna shayar da abin haifuwarsu shekara biyu cikakku ga wanda ya yi nufin ya cika shayarwa." (Suratul Baqara aya ta 233).
Hakika wannan Shine abinda ya tabbata a al-qur'ani Mai girma Cewa, a shayarda jarirai nono tsawon Shekara biyu.
Sai dai kuma Imam Ibn Qayyim al-Jawziyyah, a cikin littafensa Tuhfat al-Mawdood bi Ahkaam al-Mawlood (littafen da ke bayani tun daga haifuwa har zuwa tarbiyantarwa).
A shafi na 16 yana Cewa, "Abune mai kyau Uwa ta shayarda danta ruwan Nono kwana biyu ko ukku da haifuwa, Saboda yana dauke da wasu sinadirai wanda bayan kwana biyu ko ukku da haifuwa ba za'a same su a jikin mahaifiya ba"
Ibn Jawziyyah yace, "Dukkan larabawa sun tafi akan wannan al'ada, basu kai 'ya'yansu wani wuri wajen shayarwa har sai Bayan kwana Biyu ko Ukku, kamar yanda ya faru da Annabi (Saww) bayan ya sha nono aka bada shi Raino ga Banu Sa’d"
Wannan Shine abinda Ni dai na san yazo addinance amma kuma don an shayarda Jariri ruwan nono tsawon wata Shidda ba laifi bane a musulunci. Makawar anga likita kwarare kuma amintacce yayi bayani akan wannan shayarwar bata da Illah a lafiyar Jinjiri.
Amma kuma mu Binciken da mukayi bamu ga wata Illah ga wannan shagarwar ba domin Likitoci sun tabbatar da A Cikin Wannan ruwan Nono na mahaifiya to akwai duk abinda yaro yake nema na ci ko sha a ciki.
Wallahu A'alam