MAHAIFI NANE YA TSAIDAMIN MIJIN AURE KUMA WALLAHI MALAN KO KAƊAN BANA QAUNAR MUTUMIN HAKAN TASA ZUCIYATA NA TAMUN SAQESAQIN MUGAYE ABUBUWA AKANSHI



MAHAIFI NANE YA TSAIDAMIN MIJIN AURE KUMA WALLAHI MALAN KO KAƊAN BANA QAUNAR MUTUMIN HAKAN TASA ZUCIYATA NA TAMUN SAQESAQIN MUGAYE ABUBUWA AKANSHI

*TAMBAYA*❓

Aslm malan Allah shiqaramaka lpy Dan Allah malan inaneman shawara da Kuma baran addu,a wlh malan inacikin matsala mahaifinane ya tsaidamin mijin aure Kuma wlh malan kokadan bana qaunar mutumin hakan tasa zuciyata natamun saqesaqin mugaye abubuwa akanshi kuma Dan Allah malan katayani addu,a wlh Allah yajarabeni da son wani ammashi bayasona mun Dade taredashi saiyanzu yajuyamin baya Kuma nakasa cireshi araina Dan Allah malan kataimakamin


*AMSA*👇


To agaskiya ya kamata iyayenmu ku sani damar da shari'a ta baku wajen aurar da ýaýanku mata baya nufin kuyi musu auren dole domin babu auren dole a addinin musulunci Hadisin da Annabi ﷺ yace daku *IDAN WANDA KUKA YARDA DA ADDININSA DA 'DABI'UNSA YA ZO MUKU (NEMAN AUREN ÝAR KU ) TO KU AURA MASA* baya nuna cewa ku tilasta mata dole sai ta aureshi a'a idan ma tarbiyyarsa saurayince tasa kuke son aura mata shi to rarrashinta zakuyi ku kwaďaitar da ita hikimar auren mutumin kirki sannan ku basu dama su fahimci juna,idan kuma tana da wanda take so to abinda zakuyi shine kuyi binkice akansa idan yana da nagarta to sai ku aura masa ita, idan kuma bashi da nagarta to kar ku yadda ku aura masa ita duk yadda take son sa domin umartarku da akayi na ku aura mata mutumin kirki yana nuni ne da kar ku aura mata mutumin banza domin aurar da ita ga mutumin banza koda suna son juna tabbas babu abinda hakan zai haifar anan gaba sai dai ma nadamar da ba zatayi amfani ba.

*WANI MAHAIFI YA YIWA ÝARSA AUREN DOLE A LOKACIN MANZAN ALLAH ﷺ SAI TAKAI KUKANTA GURIN MANZON ALLAH ﷺ SAI MANZON ALLAH YA BATA ZA'BI MA'ANA IDAN TANA SON SA TAJE TA ZAUNA DASHI IDAN KUMA BATA SON SA SAI A RABA AUREN, SAI ITA MATAR TACE TA AMINCE DA ZA'BIN MAHAIFINTA AMMA DAMAN TANA SON MATA SU SANI IYAYENSU BASU DA IKON SUYI MUSU AUREN DOLE* to baiwar Allah akwai wani darasi da nake son ki dauka a cikin hadisnin wannan baiwar Allah Domin ita ta Amince da auren dolen da mahaifinta yayi mata ne a sakamakon mijin da mahaifin ya aura mata mutumin kirki ne,sabida idan ba mutumin kirki bane babu yadda za'ayi ta amince da zabin mahaifin nata, Sabida haka ni shawarar dazan baki shine lallai kiyi nazari matukar mutumin da mahaifinkin ya zaba miki mutumin kirkine to kije kiyi *Istikhara* (Sallar neman zabi) idan kinji ya kwanta miki a rai to kawai ki amince ki aureshi domin a gaskiya na fahimci rashin mayar da al'amarinki ga Allah madaukakin sarki da kuma illar da wancan ďan yadaurar yayi miki shi yasa kika shiga wannan halin har zuciyarki take miki saqe-saqe marasa kyau akan za'bin mahaifinki, kenan ya kamata kisan me kike yi lallai ki tara hankalinki waje daya ki dogara ga Allah ki dage da addu'ar Allah ya sauqaqa miki wannan yanayin da kike ciki ya kawo miki mafita, Allah madaukakin sarki yana cewa:
* ﻭَﻣَﻦ ﻳَﺘَﻮَﻛَّﻞۡ ﻋَﻠَﻰ ﭐﻟﻠَّﻪِ ﻓَﺈِﻥَّ ﭐﻟﻠَّﻪَ ﻋَﺰِﻳﺰٌ ﺣَﻜِﻴﻢٞ *
*KUMA WANDA YA DÕGARA GA ALLAH, TO, LALLE NE ALLAH MABUWÃYI NE, MAI HIKIMA.* (Sura Al-Anfal, Ayah 49)

A wata ayar kuma madaukakin sarki yake cewa:
* ﻭَﻣَﻦ ﻳَﺘَّﻖِ ﭐﻟﻠَّﻪَ ﻳَﺠۡﻌَﻞ ﻟَّﻪُۥ ﻣَﺨۡﺮَﺟٗﺎ *
*KUMA WANDA YA BI ALLAH DA TAƘAWA, ALLAH ZAI SANYA MASA MAFITA.* (Sura At-Talaq, Ayah 2)
Sabida haka wannan hanyar ita kaďai zaki bi ki samu mafita Maganar wancan mayaudarin daya juya miki baya to itama dai Addu'a zakiyi Allah ya sauqaqa miki ya cire miki sonsa a kikin zuciyarki masamman ma daman son da ya nuna miki na karyane kinga kenan yaudararki yayi ba da nufin aure ya so ki ba, Allah ne ma ya zabeki rabuwarku tazo karshe wata'kila yabi duk hanyar da zaibi ya cutar dake bai samu dama ba shi yasa ya juya miki baya, Sabida haka idan ma kina tuna yanayin da kuka kasance da juna a baya na kalamai masu shau'ki na soyayyar *wucin gadi* to yanzu yakamata ki gane kalaman a iya baki ne ba sukai cikin zuciya ba domin da sunkai har cikin zuciyarsa inaga zeyi wuya ya juya miki baya.

A karshe kuma ki sani *IDAN KIKA NEMI ABOKIN ZAMA WANDA KIKE SO TO ZAI ZAMAR DAKE KAMAR BAIWA IDAN KUMA KIN ZA'BI ABOKIN ZAMA WANDA YAKE SON KI TO ZAI ZAMAR DAKE KAMAR SARAUNIYA* Amma bana nufin kar ki auri wanda kike son sa yake son ki a'a ina nufin kar ki auri wanda kike son sa baya son ki, Sabida haka kiyi nazari indai wanda mahaifinki ya zaba miki yana matukar son ki kuma yana da addini da kyauwun hali lallai ina mai baki shawara ki aureshi domin zai baki kulawa Sama da wancan mayaudarin da kike ta tunani.
Ammafa idan duk kinbi hanyoyinnan amma ba kiji son sa a ranki ba to gaskiya kije ki sanar da waďanda kika san mahaifinki yana Jin maganarsu ki sanar dasu cewa ke fa bakya son saurayin naki insha Allahu Zasu fahimceki kuma zasu fahimtar dashi illa da hatsarin yiwa ýaýa auren dole****

Wallahu A'alam

ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ , ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ
idan Anga Gyara A Sanar Damu
=
=
*MASU YANKE MANA RUBUTU KUJI TSORON ALLAH, DUK WANDA YA CIRE MANA KODA HARAFI 'DAYA NE, TO BAMU YAFE BA ALLAH ZAI MANA HISABI MU DASHI A RANAR SAKAMAKO*

Na So Kun San Tarin Lada Da Albarka Da Ake Samu Ta Hanyar Yada Ilimi Ko Wani Alkhairi
=
=
POSTED ADDINI DA RAYUWAR DAN ADAM GROUP Fadakarwa Nishadantarwa Manufarmu Shine Yada Ingantattun Darussa Na Addini Tare Da Wayar Da 'yan Uwa Al'amuran Zamantakewa Na Rayuwa .
Post a Comment (0)