MANYAN ZUNUBAI GUDA BIYAR MASU JANYO FARI DA RASHIN SAUKAR RUWAN SAMA
Saukar ruwan sama ni'imace daga cikin ni'imomin Allah Ta'ala, rashin saukar ruwa a lokacin da bayi ke bukatar sa azabace da Allah yake jarabta bayinsa sanadiyyar zunubansu, don su tuba su koma ga Allah kuma Allah ya tsarkake daga laifukansu tun daga nan duniya.
Babban abinda yake janyo rashin ruwan sama shine yawaita ZUNUBAI da ake yi a bayan kasa, malamai sun fitar da manyan ZUNUBAI guda biyar waɗan da suke janyo rashin saukar ruwan sama
*_1-Garman kai a bayan kasa da nuna rashin tausayi ga bayin Allah, da alfahari da dukiya da abin duniya, da rashin adalci na shuwagabanni_*.
Ruwana sama yana sauka ne sanadiyyar ƙankan da kai zuwa ga Allah, da kuma nuna tausayi da jin kai ga bayin Allah da kuma sauran halittun Allah
Allah yana cewa
﴿وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا إِلَى أُمَمٍ مِنْ قَبْلِكَ فَأَخَذْنَاهُمْ بِالْبَأْسَاءِ وَالضَّرَّاءِ لَعَلَّهُمْ يَتَضَرَّعُونَ * فَلَوْلَا إِذْ جَاءَهُمْ بَأْسُنَا تَضَرَّعُوا وَلَكِنْ قَسَتْ قُلُوبُهُمْ وَزَيَّنَ لَهُمُ الشَّيْطَانُ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ﴾
Ma'ana:
*_(Kuma lalle Mun aika zuwa ga al´ummai daga gabãninka, sai Muka kãmã su da tsanani da cũta, tsammãninsu zã su ƙanƙan da kai, To, don me, a lõkacin da tsananinMu ya jħ musu ba su yi tawãlu´i ba? Kuma amma zukatansu sun ƙħƙashe kuma shaiɗan yã ƙawãta musu abin da suka kasance sunã aikatãwa)_*.
@الأنعام: 42، 43
ابن عباس رضي الله عنه:
Yana cewa:
"Manzon Allah SAW ya fito zuwa ga Sallar roƙon ruwa yana mai ƙanƙan da kai, tare da nutsuwa da tsoron Allah tare da nuna matukar buqata zuwa ga Allah..."
@صحيح سنن الترمذي.
*_2-Yaɗa ɓarna a tsakanin mutane, idan yaɗa sabon Allah da laifuka yayi yawa a tsakanin mutane, to Allah yana jarabtar mutane da rashin ruwan sama_*.
Manzon Allah SAW yana cewa:
(Ya ku taron jama'ar masu Hijira, waɗan su halaye guda biyar idan aka jarabceku da su, ina rokon Allah kada wannan abu ya riske ku, sannan sai Manzon Allah SAW ya ambace su sai ya ambaci:
*_Mutane baza su riƙa Tauye mudu ko abin awo ba face sai Allah ya jarabce su da shelaru na fari da rashin ruwan sama.....)_*
@صحيح سنن ابن ماجة.
*3-Karyata Ayoyin Allah da sabawa Annabawan Allah_*
Rashin ruwan sama azaba ce da Allah ya yi gargadi ga mutanen Fir'auna akan karyata ayoyin Allah da suka yi, Allah yana cewa:
{ولقد أخذنا آل فرعون بالسنين ونقص من الثمرات لعلهم يذّكرون}.
Kuma irin wannan azabar ta rashin ruwan sama Manzon Allah SAW ya roƙi Allah ya jarabci Quraishawa da ita lokacin da suka karyata Manzon Allah SAW ko sun ji gargadin Allah.
Daga Abdullahi bn Mas'ud R.A yace:
"Lallai Quraishawa sun ci galaba akan Manzon Allah SAW suka nuna zalunci da karyata Manzon Allah SAW, sai Manzon Allah SAW yace:
*"اللهم أعني عليهم بسبع كسبع يوسف"*
Ya Allah ka taimake ni akan su ta hanyar sanya masu shekarun bakwai na fari da rashin ruwan sama kamar yadda kayiwa mutane Annabi Yusuf, sai Allah ya jarabce su rashin ruwan sama suka riqa cin mushe har yunwa ta sanya suke ganin hayaƙi daga sama..........)*
@البخاري.
Allah ne mafi sani.
SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/DailyHadithss