💎🍁💎🍁💎🍁💎🍁💎🍁💎🍁
MUJALLAR FINA-FINAN INDIYA
💎🍁💎🍁💎🍁💎🍁💎🍁💎🍁
KE GABATAR MUKU DA SHIRIN
༄🌼༄🌼❄️✿🌀...♡...🌼༄🌼༄
MATA A FINA-FINAN INDIYA
༄🌼༄🌼❄️✿🌀...♡...🌼༄🌼༄
Kashi na (02)
Tare da
•----------•✬(✪)✬•----------•
Haiman Raees
•----------•✬(✪)✬•----------•
•┈┈••♡🍃♡••┈┈•
3rd August 2021
•┈┈••♡🍃♡••┈┈•
Tsiraici A masana'antun fina-finan Indiya.
Kamar yadda na kawo rabe-ben irin halaye ko ɗabi'un da mata kan fito a ciki a fina-finan Indiya. In kuka yi duba da kyau za ku ga cewa a yau mafi yawancin fina-finan da matan ke fitowa a ciki suna fitowa ce da shiga ko siffa ko hali kwatankwacin na matan da ke fitowa a cikin fina-finan turai. Misali; sau da dama ana nuna matan nan a fina-finai a matsayin ababen marmari ne kawai da sha'awa, wannan shi ya jawo tasgaro game da soyayya da kuma yadda ake bayyana mata a masana'antun fina-finan ƙasar Indiya.
A da, ba a san wani abu wai shi 'sumba' (wato kiss) a fina-finan Indiya ba, asali ma, sai da aka ɗauki tsawon shekaru a wannan yanayi kafin a fara, amma yau fa? Abu ne mawuyaci a samu fina-finai biyar daga cikin fina-finai kusan dubu ɗaya da ake fitarwa a cikin kowace shekara daga dukkan masana'antun fina-finan Indiya wanda ba a sumba, fitsara ko kuma nuna tsiraici a ciki. A cikin fina-finan da, nuna soyayya a fili an barshi ne wa fina-finan turai kawai, amma a yau za ka sha mamakin irin yadda ake fitsara da baɗala a cikin fina-finan Indiya, abin har ya kai ga iyaye da dama a nan ƙasar Hausa yanzu ba sa iya barin 'ya'yansu su kalli mafi yawancin fina-finan saboda fitsara ko ta'addanci da ya yi yawa a fina-finan, alhali da kusan kowane gida babu abin da ake kallo sama da su.
A da, masu ruwa da tsaki wajen shirya fina-finai, musamman daraktoci. Suna amfani da hanyoyi uku ne wajen isar da saƙon soyayya ko tarayya ko alaƙa mai zurfi a tsakanin mace da namiji. Waɗannan hanyoyi kuwa su ne: shigar al'ada, mafarki da kuma bayan gari ko cikin daji. Bari in bi su ɗaya bayan ɗaya in faɗaɗa bayani.
SHIGAR AL'ADA
Kasancewar mafi yawancin fina-finan Indiya sun ƙunshi rawa da waƙa, daraktoci na amfani da shigar al'ada wajen bayyana sassan jikin mace, musamman daga cikinta zuwa ƙasan cibiyarta.
MAFARKI
Fitowar mafarki tana ba wa daraktoci damar bayyana tsiraici ko nuna yadda ake lalata ko aikata masha'a cikin sauƙi. Akan nuno mace sanye da sari, ruwan sama ko kuma na wani wuri can daban ya jiƙa mata jiki sarin ya manne da jikinta ta yadda kana iya ganin komai a bayyane, ko kuma in iska ta kaɗa ka ga ta yaye sarin komai ya fito waje. In ya so bayan an gama abin da aka yi niyya, sai a nuna wa masu kallo cewa ai duk ma a mafarki ne abin, shikenan.
BAYAN GARI KO CIKIN DAJI.
Sau da dama waƙoƙi da raye-raye na ba wa jaruman shiri damar zuwa bayan gari ko cikin daji. A irin wannan fitowa akan ga jarumar ta ruga a guje ta shiga daji, yayin da shi kuma jarumin zai bi ta a guje shi ma su shige cikin ganyayyaki, da sun fito sai a nuno ta tana goge leɓenta, daga nan kai mai kallo ka san me ya faru.
Wannan shi ne tsarin da ake bi a da wajen bayyana irin waɗannan abubuwa, to a da manya ne kaɗai ke iya fahimtar manufofin irin waɗannan saƙonnin. Kuma a hakan ma ba a wuce gona da iri, amma yanzu abin ya wuce inda ake tunani, kuma a ƙarshe dai, matan da su ake amfani wajen cimma burikan da ake so a cimma.
Zan ci gaba in sha Allah.
©️✍🏻
Haiman Raees
# haimanraees
Haimanraees@gmail.com
Miyan Bhai Ki Daring