SUNAN HUMAIRA



SUNAN HUMAIRA
:
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaikum malam na haihu nasami diya mace an sanyamata suna Aisha to sunan mahaifiyatane shine nace zankirata da.humaira to mutane dayawa suncemin humaira yana nufin jaririn jaki dan Allah malam hakane inason karin bayani dan nasami sunan kiranta yau kwananta 11
:
*AMSA*👇
:
Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

Toh Humaira ma'anarta shine 'Yar Ja, wanda asali daga Hamra'u ne, wato Ja, se akayi tasgirinsa ake cewa Humaira, wannan kuma wani salo ne na larabawa idan sunaso su qanqanta abu, ga babba ga qarami ga kuma É—an qarami toh wannan É—an qaramin shine suke tsamo sunanshi daga jikin sunan babban, misali Umar, idan kanaso kace dan qaramin Umar sekace Umair, Usman idan kanaso kace dan qaramin Usman sekace Usaimin, Salaha idan kanaso kace 'yar qaramar salaha sai kace Sulaihat, Zaliha kuma Zulaihat, toh itama Humaira asali daga Hamra'u ne wato Ja, idan kanaso kace 'yar Ja wato qaramar Ja shine sai kace Humaira, kuma wannan sunan babu laifi acikinshi domin ko acikin hausawa akwai wacce ake cemata 'yar ja kuma tana amsawa, toh ma'anar wannan 'yar ja din shine Humaira.

         Amma Aisha tasamu laqabin Humaira ne daga Bakin Annabi (s.a.w) lokacinda Aisha tatare a gidan Manzon Allah to 'yarsa Fateema ta girmi Aisha, ita kuma Aisha tana ganin kanta matsayin matar uba gakuma quruciyarda take kansu a wannan lokacin se suka riqa É—an samun sabani tsakaninsu toh shikuma Annabi (s.a.w) ko kaÉ—an bayaso a taÉ“a masa Fateema duk da cewa tafi qarfin Aisha amma sai Annabi (s.a.w) yake gayanata ke 'yar ja (Humaira) ki kiyayi fateema, toh daga bakin Annabi (s.a.w) aka samo wannan laqabin na Humaira kuma matarsa Aisha yake gayama haka kasantuwarta Ja ce kuma yarinya qarama a wancan lokacin, to daga nan aka samo kiran duk wata me suna Aisha da wannan laqabi na Humaira, kuma babu Yadda Za'ayi Annabi (s.a.w) ya sanyawa matarsa laqabi wanda ba me kyauba, dan haka babu wani laifi dan ancewa Aisha Humaira Insha Allahu

Allah yasa mudace

Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)