TURARE GA BUDURWA



TURARE GA BUDURWA
As-salamu alaikum.
*Annabi ya ce: KOWACE MACE TA SHAFA TURARE, SAI TA WUCE WASU MUTANE DON SU JI 'KAMSHINTA, TO ITA MAZINACIYA CE. [Sahi'hun Nasa'i; 5141]
*Annabi ya hana mace ta yi amfani da turaren wuta "Bakhur" idan za ta fita waje ko da masallaci ne za ta. [SAHI'HU MUSLIM; 444, FATA'WA IBNI BAZ; 10/40]
*Idan mace ta shafa turare don zuwa masallaci, to wajibi ne ta yi wanka irin na janaba. [SILSILATUS SAHI'HA; 1035, AWNUL MA'BUD; 7/259]
*Komai a ka hana manya su aikata, to haram ne a bar yara su aikata shi, zunubi ya na hawa kan waliyyan yaran, idan 'kanana ne. [SHARHU SAHI'HI MUSLIM; 7/180]
*Babu laifi ga mace ta shafa turare a zaman gida ko taron mata zalla, idan ba za ta fita waje ba. [AL-FATAWAL JA'MI-ATU LIL-MAR'A; 3/903]
Post a Comment (0)