YI MA ALLAH KIRARI DA SALATIN ANNABI SIRRIN KARƁA ADDU'A



YI MA ALLAH KIRARI DA SALATIN ANNABI SIRRIN KARƁA ADDU'A 

Manzon Allah (SAW) Ya ji wani mutum yana addu'a sabida garaje bai tsaya ya yabi Allah ba bai yi ma Annabi (SAW) salati ba ya shiga addu'a, se Annabi (SAW) ya ce, Ka yi garaje ya kai wannan mai sallah, sannan Annabi ya koyar da shi, ka tsaya ka yi ma Allah yabo da kirari ka yi ma Annabi (SAW) salati. Sannan (Annabi) ya ji wani yana sallah ya yabi Allah (ya kwarzanta shi) ya masa kirari ya gode masa, ya kuma yi ma Annabi Salati (SAW), Sai Annabi (SAW) ya ce da shi, to ka yi Addu'a za'a amsa maka kuma ka tambaya za'a baka. - Abu Dawud, Nasa'i, Tirmizi.

Note:
Allah Ta'ala yana son yabo da kirari da kansa Allah Ta'ala ya yabi kansa, Yana daga cikin SIRRIN karɓa addu'a fara yi ma Allah kirari da gode masa da kuma yi ma Annabi SALATI da rashin gaggawa. Allah ka amsa mana idan mun roƙe ka.

# Zaurenfisabilillah

TELEGRAM: https://t.me/Fisabilillaaah

FACEBOOK:
https://www.facebook.com/Zaurenfisabilillah-107455768160058/?ti=as
Post a Comment (0)