ZUNUBIN DA ALLAAH BAI YAFEWA



ZUNUBIN DA ALLAAH BAI YAFEWA

*TAMBAYA*❓

Slm mlm anwuni lpia  mlm inada tanbaya mlm akwai zunubin da Allah baiyafewa aduniya koka tuba???

*AMSA*👇

_Laifin *Shirka babba* shi ne wanda Allah (ﷻ) ba Ya yafewa. Saboda fadin Sa:_

_*”إِنَّ اللَّهَ لَا يَغفِرُ أَن يُشرَكَ بِهِۦ وَيَغفِرُ مَا دُونَ ذَٰلِكَ لِمَن يَشَآءُ وَمَن يُشرِك بِاللَّهِ فَقَدِ افتَرَىٰٓ إِثمًا عَظِيمًا“* [ النساء: ٤٨]_

*“Lalle ne Allah ba ya gafarta a yi shirka gami da shi, kuma amma Yana gafarta abinda yake bayan wannan ga wanda Ya so, kuma wanda ya yi shirka da Allah, to lalle ne ya kirkiri zunubi mai girma.”* (Suratun Nisa’i: 48).

_Wannan ayar na nuna duk wanda ya haɗu da Allah alhali ya mutu yana Shirka, to Allah ba zai gafarta masa ba, kuma wuta ita ce makoma a gare shi._

_Amma idan mutum ya yi tuba, tuba kebantacciya tun a duniya kafin ajalinsa, to Allah Mai yawan gafara ne, Zai iya yafe masa idan Ya so._

_Babu wani laifin da ya tabbata cewa idan mutum ya tuba tun a duniya Allah ba zai amshi tubar shi ba. Ni dai ban san wannan laifin ba._

_Wallahu a'lamu._

_*✍🏿Ayyoub Mouser Giwa.*_
_*08166650256.*_

Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)