SALLAR SHAFA'I DA WUTIRI



SALLAR SHAFA'I DA WUTIRI

*TAMBAYA*❓

Assalamu alaykum
Zan iya yin sallar shafa'i da wutiri da zarar na idar da sallar isha?

*AMSA*👇

Babu laifi idon Mutum yayi sallarsa ta shafa'i da wutiri bayan Isha'i, domin an ruwaito. Hadisi na bukhari mai Lamba 996, Nana Aisha Allah ya qara Mata yarda tace, manzon Allah ya kasance yakanyi sallarsa ta wutiri a cikin ko wane 6angare na dare, wani lokacin a farkon dare, wani lokacin a tsakiyar dare, wani lokacin a qarshen dare kafin asuba, don haka idan Mutum yana gudun Mantuwa ko Makara sai yayi sallarsa da wuri babu Laifi.
Amma duk wanda Mutum ya dauka yayi, saidai ita wutiri itace makulli ga duk wata sallah, watau bayan wutiri ba'a yin wata sallah sai da asuba.

Allah ne mafi sani

Jameelu Maska

Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)