HUKUNCIN WANDA YAYI RANTSUWA BA ZAI AIKATA WANI ABU BA



HUKUNCIN WANDA YAYI RANTSUWA BA ZAI AIKATA WANI ABU BA :

TAMBAYA TA 2730
***************
Assalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu malan barka da qoqari Allah yasaka da alkhairi yaqara ilimi da basira yasa fadakarwan nan ta anfani musulmi baki daya Allah yahada fuskokinmu acikin aljanna ameen.
Bayan haka malan tambayata itace ina zaune tare da kakata da qannen mahaifina da 'ya 'yan qanwar babana a gidansu mahaifina nagado to sai yaxamana abubuwa suka riqa faruwa na nuna banbance har takai nakasa haqura nabar gidan tare dayin alqawarin baxan sake xuwa na kwanaba konayi wani Abu sai dai idan ita kakar tamuce batada lfy daga baya nayi rantsuwa to bayan haka kuma sai suka nemi araba gadon aba kowa nasa sai mahaifina yasiya gidan to shine nake tmby ya ya hukuncin rantsuwa da alqawarin danayi nacewa baxan qara kwana a gdn ba?
Ngd

AMSA
***
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Tunda kin riga kinyi rantsuwa cewa ba zaki sake komawa gidan da niyyar kwana ba, sai dai idan kakarki ce bata da lafiya, to yanzu kuma tunda wajen ya zama mallakar mahaaifinki shine kike so ki sake komawa da kwana agidan, to ya halatta ki koma din amma kuma wajibi ne akanki kiyi kaffarar rantsuwar nan da kikayi.
Manzon Allah ( ï·º ) yace : "Idan kayi rantsuwa akan wani abu, kuma sai daga baya kaga cewa waninsa shine yafi alkhairi gareka, to kaje wa abinda yafi alkhairi din sannan kayi kaffarar rantsuwarka".
(Sahihul Bukhariy hadisi na 6622, Abu Dawud hadisi na 3277, Sahihu Muslim acikin kitabul Iman).
Kuma yadda yazo acikin ayah ta 89 acikin Suratul Ma'idah, yadda zakiyi kaffarar shine : Ki ciyar da miskinai guda goma, ko ki tufatar dasu, ko kiyi azumin kwana uku, ko kuma 'yantar da baiwa ko bawa.
Idan ciyarwar zakiyi, to zaki ba ma kowanne miskini gwargwadon mudun Nabiyyi ï·º biyu ne. Wato misalin rabin karamin kwanan-sha na danyen abinci, dawa ko masara ko Shinkafa ko gero.

WALLAHU A'ALAM.

DAGA ZAUREN FIQHU
07064213990

Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)