ANNABI DA SAHABBANSA // 074



ANNABI DA SAHABBANSA // 074
.
Mawallafi: Baban Manar Alqasim
.
Abu-Dujana jarimi ne na qin qarawa, har yana da wani jan qyalle da yake daurawa a kai, da zarar ya daura mutane za su gane cewa yaqi zai yi sai dai mutuwa, don haka yana amsar takobin daga Manzon Allah SAW ya daura wannan qyallen ya keta sahu cikin izza, wanda a nan ne Annabi SAW yake cewa "Irin wannan tafiyar ce Allah SW yake fushi da ita in ba a irin wannan wurin ba" Arraheeq Almakhtuum P180.
.
Su kuwa mushrikai suka shirya rundunarsu a tsarin sahu-sahu, wanda yake babban kwamanda a lokacin Abu-Sufyan ne, shi ne yake tsakiyar rundunar, a dama kamar yadda muka fadi suka sanya Khalid bnl Waleed (Sannan bai riga ya zama babban kwamandan rundunar muslunci ba) ta hagu kuma suka dora Ikrima bn Abijahal, wanda ya jagoranci sojin qasa kuma shi ne Safwan bn Umayya, kwamandan masu harbi da kibau kuma suka dora Abdillahi bn Abi-Rabee'a.
.
Sai aka miqa tuta a hannun jagororin Banu Abdid-daar, da ma su suke riqe da wannan matsayin tun lokacin da aka raba matsayin da suka gada daga Qusay bn Kilaab a tsakanin qabilunsu, sai da gangan Abu-Sufyan ya harzuqo su don ya motsa su yadda ransu zai baci sosai su tsaya don kare mutuncin qabilar, duk sun san cewa an qwace tutar a Badar ta yadda aka damqe mariqinta wato Nadr bnl Harith, sai ya tuna musu.
.
Yake cewa "Ga shi Banu Abdid-Daar ku aka damqa muku haqqin kula da tutarmu a yaqin Badar, to ga irin abin da ya faru da mu nan, kun san ba a iya gamawa da mutane sai ta hanyar tutarsu, ana gamawa da ita su kuma tasu ta qare, don haka ko dai ku kare mana tutarmu, ko ku bar mu da su mu yi maganinsu, ba shakka ya ci nasara, don kuwa sun yi matuqar hasala, har da nuna yatsa suna cewa "Mu ne za mu ba ka tutarmu? Allah ya kai mu gobe ka ga abin da za mu yi, sun yi mutuqar kafewa har sai da aka qarar da su.
.
TURKA-TURKAR SIYASA GABANIN YAQI
Dab da gwabzawa Quraishawa suka yi qoqarin jefa rabuwar kai a tsakanin musulmai, yadda Abu-Sufyan ya aika wa Ansarawa da saqon cewa "Shi wannan dan uwanmu ne ku bar mu da shi, mu kuma mu fita harkarku ba kare bin damo" irin wannan maganar ba wani tasirin da za ta yi wa muminai masamman sahabban Annabi SAW, sai ma suka narka masa mummunar amsar da ta dame shi, duk da haka ba su yi qasa a gwiwa ba dab da fara yaqin suka sake saqa wani ta hanyar Abu-Amir amma ba su yi nasara ba.
.
QOQARIN DA MATANSU SUKA YI
Tabbas su ma matan Quraishawa sun taka irin tasu rawar wajen yaqi a gefen mazajensu, inda suka sa wata mai qoqarin cikinsu ta riqa jagorantarsu, suna datsa tsakiyar sahu-sahun mazajensu suna buga mandiri don zaburar da su, da fito da jarumtarsu, yadda kowa zai yi yaqin ko a mutu ko a yi rai, suna waqa irin ta 'yammatan gada, wani lokacin ga kwamandoji, wani sa'in ga sauran mayaqan.
.
FARKON ARANGAMAR
A hankali dai har sassan guda biyu suka kusanci juna, aka fara some-somen yaqi, wanda ya fara motsi kuwa shi ne madaukin tutarsu wato Talha bn Abi-Talhal Abdariy wanda ya rako Ummu-salma Madina, yadda ya matso gaba a kan raquminsa, ba shakka daya ne daga cikin gwarazansu, ya nemi wani ya fito masa a cikin musulmai, amma sabo da sanin jarumtarsa sai wasu daga bangaren musulman suka fito, amma Zubair RA ya koma da su ya fito masa ya kuma far masa har sai da ya kai shi qasa ya yi masa yankar rago.
.
Daga nan yaqin ya barke, har ma ya watsu a duk sansanin guda biyu, amma mushrikai ga alama sun fi jin jiki, Banu Abdil-Dar ne dai ke riqe da tuta, ana kashe Talha bn Abi-Talha dan uwansa Abu-Shaiba wato Usman bn Abi-Shaiba ya amshe yana waqa, amma Hamza bn Abdilmuttalib ya fito masa, kan ka ce haka ya tsaga shi biyu, sai Abu-Sa'id bn Abi-Talha ya daga, shi ma Sa'ad bn Abi-Waqqaas ya jefe shi da mashi a wuya ya kai shi lahira, amma wasu sun ce Aliy RA ne ya kashe shi da takobi.
.
Sai Masafa bn Talha bn Abi-Talha ya daga tuta, shi ma Aasim bn Thabit bn Abil-Aflaah ya kai shi lahira da mashi, shi ma dan uwansa Kilaab bn Talha bn Abi Talha ya daga, Zubair bn Auwaam ya kashe shi, dan uwansu Jallaas bn Talha bn Abi-Talha ya daga, Talha bn Ubaidillah ya soka masa mashi, ya kashe shi, wasu suka ce Aasim ne ya harbe shi da mashi, ya gama da shi, wadannan shidan duk 'yan gida daya ne, gidan Abu-Talha, wato Abdullah bn Usman bn Abdid-Daar

Zamu chigaba da yardar Allah...

Rubutawa:- Baban Manar Alqasim 
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 

Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)