ANNABI DA SAHABBANSA /75



ANNABI DA SAHABBANSA /75

Mawallafi: Baban Manar Alqasim
.
A taqaice mutum 10 ne daga Banu Abdid-Daar kuma an kawar da su gaba daya, sai ya zamanto dole dai riqe tutar ya fita daga gidan gaba daya, koda yake wani bararren bawansu Bahabashe wanda ake kira Sawwab ya daga tutar, kuma an fadi irin gudummuwar da ya bayar wace magabatansa ba su ba da irinta ba ko kadan, a haka har aka yanke hannayensa amma sai da ya daga ta da wuyarsa da qirjinsa don dai kar a zo a rasata, a qarshe dai aka kashe shi kuma ba a sake samun wanda ya daga ba, akwai amfanoni da yawa tattare da daga tutar nan a wurin yaqi.
.
Ciki har da kasancewar in abu ya rincabe mutane ba sa sanin inda junansu suke, da haka sai wani ya fada dandazon abokan gaba bai sani ba, kuma gaba daya an rasa matsaya kenan don ba wata hanyar da za a sami sararin tattaruwa wuri guda, shi ya sa mayaqa sukan yi qoqarin kai mai riqe da tutar lahira tun a matakin farko don cin-ma wancan manufar, ba shakka muslunci ya sami babban nasara tun daga wannan lokacin, don duk an kutsa cikin mushrikai ba abin da ake musu sai kisa, don sun riga sun rikice abu ya fita daga hannunsu.
.
A daidai wannan lokacin ne Abu-Dujana ya keto da daurin kansa ja, yana riqe da takobin Manzon Allah SAW, ba abin da yake yi sai cika aiki, har dai ta kai ga bai haduwa da kafuri sai ya kai shi lahira, Zubair bnl Auwaam yake cewa lokacin da na nemi Annabi SAW ya ba ni takobin nan bai ba ni ba ya ba Abu-Dujana duk da kasancewar ni da shi dan mace ne da dan namiji na ji abin a zuciyata don ni dan Safiyya ne babarsa kuma Baquraishe".
.
Ya ce "Kuma ni na fara tambayarsa kafin Abu-Dujana, amma Annabi SAW ya ba shi ni ya hana ni, ni kuwa na ce wallahi sai na ga abin da zai yi da takobin, na riqa bin sa ina kula da shi, ya ciro jan qyallensa ya daure kansa da shi, har Ansarawa suka riqa cewa ya yi shirin mutuwa, nan ya riqa ka da maza, to akwai wani jarumi cikin mushrikai shi ma bai haduwa da wani mai rauni cikin musulmai sai ya kashe shi, na riqa tsuwurwurin su hadu, ai kuwa suka hadu din.
.
Nan fa suka kai wa juna sara, har takobin mushrikin ya kuskure Abu-Dujana, Allah SW ya taimake shi ya kare sarar da garkuwarsa, sai shi ya yi saurin kai masa nasa dukar ya kai shi lahira (Ibn Hisham 2/68-69) daga nan Abu-Dujana ya kutsa sahun mushrikai, cikin wadan da ake maganar jarumtarsu har da Hamza bn Abdilmuttalib baffan Annabi SAW, don in za a yi maganar gwaraza dole a ambato shi.
.
HAMZA RA YA YI SHAHADA
Wani abu da zai daure maka kai dangane da 'yan Shi'a, shi ne, suna zagin manyan sahabban nan da suka yi hidima don daukaka wannan addinin ne da hujjar cewa wai su ne suka cutar da ahlubaitin Annabi SAW, to an kashe Ahlul-baitin Annabi SAW yana da rai, ba ma cutarwa ba kisa, kowa ya san matsayin Hamza RA a musluncin ma gaba daya ba ma a wurin Annabi SAW ba, haka aka ba Wahshiy kwangilar kisarsa.
.
Tabbas ya cika aikinsa, ya dawo ya muslunta ya zauna tare da musulmai, ba wani wanda ya far masa ko ya tsane shi, bare a yi ta zaginsa don ya kashe ahlul baiti, ko a ajiye qabarinsa ko yaushe a riqa ziyarta ana tsine masa, to kalli yadda 'yan Shi'a suka mai da tsine wa manyan muslunci addini, suka canja addinin tun daga tushe, suka qirqiri qarairayi na cutar da ahlul baiti don sanya qiyayya da gaba a zukatan musulmai, tsakani da Allah wadannan yaqoqi da ake yi mutum guda yake yi? Akwai wata alama koda kuwa qanqanuwa ce da take nuna cewa Annabi SAW bai da natsuwa da sahabbansa? 
.
In akwai munafurci ashe Allah SW ba zai tona asirinsu kamar yadda ya yi wa Ibn Ubay a wannan yaqin ba? Roqonmu dai Allah SW ya kare mu da 'ya'yanmu da wannan bala'i na Shi'a, Wahshiy dai ya muslunta kuma ahlul baiti sun kame bakinsu ba wanda ya auka masa, tarihi da hadisai ingantattu sun nuna zafin da Annabi SAW ya ji, har ya tambayi Wahshiy yadda ya kashe baffansa amma ba wani abin da ya ce a yi masa, Allah ya raba mu da Shi'a.
.
Wahshiy yake cewa "Lokacin da nake bawa a hannun Jubair bn Mut'im ne yake ce min "In ka kashe Hamza baffan Muhammad na 'yanta ka" to dama an kashe baffan Mut'im din ne a Badar, wato Tu'aima bn Adiy, shi ne yake son shi ma a kashe baffan Annabi SAW din don ya dauki fansa, Wahshiy da kansa yake cewa shi bawa ne Bahabashe, ya iya jifa da mashi kamar yadda suke yi a Habasha, zai yi wahala ya nufi abu ka ga bai same shi ba, don haka lokacin da mayaqan suka fito na yi ta neman Hamza RA.

Rubutawa:- Babban Manar Alqasim 
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)