INA SONTA KAMAR YADDA TAKE



'INA SONTA KAMAR YADDA TAKE.

Wata mata ta bukaci mijinta da ya rubuta halayenta mara kyau da yake fatan ta canza su, da mijin ya karba takardar bai rubuta komai ba face, ✍inason matata kamar yadda take, banga wani aibi a tareda 'ita ba, Sai yabata takardan a nade.

Bayan mijin ya fita da matar ta karanta sai farinciki ya lullubeta ta shirya lillinka kyautatawa ga mijinnata saboda tsananin farinciki. 🌹

Mijin yace, inada kurakurai sama da goma da matata take aikatawa, amma ni na sani cewa ambatonsu bazai taba zama dalilin gyarasu ba har abada👌saidai nasan ta dalilin yaba mata da boye aibunta zai 'iya sa tacanza daga abinda bana so din cikin qanqanin lokaci.

Kasani ambaton aibu sau dayawa yana sa rashin jin dadi, ya tafi da farinciki, ya saka rashin walwala musamman in agaban mutane ne.

Amma kuma shi yabo, yana karo so da kauna da nishadi hade da jindadi, kuma dalili ne na samun Karin kyautatawa daga abokin zama.

Tuna fadan Allah madaukakin sarki inda yake cewa.
(وقولوا للناسِ حسنا )
(ألم تر كيف ضرب الله مثلا كلمة طيبة كشجرةٍ طيبة أصلها ثابتٌ وفرعها في السماء)

'Ita dai kalma mai kyau sadaka ce🌹🌹 Allah yasa mudace.
Post a Comment (0)